Tsaftar Muhalli: An Kama Mutane 111 da karya Dokar tsaftar Muhalli a Kano

Date:

  1. Daga Sani Abdulrazak Darma
Gwamnatin Jihar Kano ta bayyana cewar a shirye take ta cigaba da bayar da kulawa ga Al’umma domin kula da Muhallan su.
Kwamishinan Muhalli  Dr Kabiru Ibrahim Getso ne ya bayyana hakan, yayin zagayen Tsaftar Mahalli na karshen wata-wata.
Dr Kabiru Getso yace Gwamnatin Dr Abdullahi Umar Ganduje ,ta himmatu wajen tsaftace Muhalli domin kawar da Duk wata cuta da take yaduwa a cikin Al’umma.
Kwamishinan Muhallin yace an Samar da wannan tsari na gyara Muhalli na karshen wata ne, domin Al’umma su zauna a Gidajen su, don kawar da duk wata kazanta da take tattara a Mahallan al’umma.
Wakilin Kadaura24 Sani Abdurrazak Darma ya rawaito mana cewa yayin gudanar da zagayen Tsaftar Mahallin, an samu mutane 111 wadanda suka karya doka Kuma aka ci tarar su kudi naira 123,200 Wanda kotun tafi da gidan ka suka kama.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Kamata ya yi wajen Mauludi ya Zama waje Mai nutsuwa saboda ana ambaton Allah da Manzonsa – Mal Ibrahim Khalil

Shugaban Majalisar shuhurar Malamai ta jihar Kano Sheikh Malam...

Ra’ayi:‎Tsarin Kwankwasiyya ya dora Kano a gwadaben cigaba a mulkin Gwamna Abba Kabir -Adamu Shehu Bello

‎ ‎Ra’ayi ‎ ‎Daga Adamu Shehu Bello (Bayero Chedi), Jigo a Kwankwasiyya...

Al’ummar Garin Riruwai da wani Kamfanin Hakar ma’adanai Sun Cimma Yarjejeniya Kan Ci gaban yankin

Kwamitin ci gaban Al’ummar garajn Riruwai da wani kamfanin...