Daga Aliyu Danbala Gwarzo
Jami’an hukumar Hisbah ta jihar Kano sun kama wani matashi dan shekara 24, wanda ya fito a wani bidiyo ya na ‘lasar’ al’aurar akuya, domin neman shahara a shafukan sada zumunta.
Majiyar jaridar kadaura24 ta Daily News 24 ta ruwaito cewa an kama yaron ne mai suna Shamsu Yakubu, mazaunin karamar hukumar Dawakin Kudu da ke jihar a ranar Talata.
A cikin faifan bidiyon, wanda ya yadu a shafukan sada zumunta, musamman Tiktok, an ga Yakubu yana umurtar wani da ya dauki hotonsa yana a kan lasar al’aurar dabbar .

Ya bayyana cewa yana ya yi hakan ne saboda yana neman daukaka a shafukan sada zumunta .
Sai dai mazauna yankin da suka fusata da wannan mummunar dabi’ar ta Yakubu, sun yi yunkurin yi masa dukan tsiya, wanda hakan yasa wani mutum a yankin ya mika matashin ga Hukumar Hisbah, inda nan take ta kama shi.
Sai dai a wata tattaunawa da jami’an Hisbah a birnin Kano, Matashin ya musanta cewa ya lashi al’aurar dabbar, inda ya ce ya dora bakinsa ne kawai a al’aurar akuyar.
Yanzu-yanzu: Ganduje ya magantu kan batun komawar Kwankwaso APC
“Na rantse da Allah ban lashi al’aurar akuya ba, kawai na sanya bakina a wajen,” in ji shi.
“Ban taba yin irin wannan abu a baya ba, ina cikin hayyacina, wannan ne karo na na farko kuma ba zan sake yin hakan ba, in ji shi,
Sai dai hukumar Hisbah ta ba da umarnin a yi wa matashin gwajin kwakwalwa ko yana da tabin hankali.
Matashin ya kuma ce shi baya shaye-shayen miyagun kwayoyi.
Da yake zantawa da manema labarai kan batun, Mataimakin Babban Kwamandan Hukumar Hisbah, Sheikh Aminuddeen Abubakar, ya ce kafin a hukunta matashin za a yi masa gwaji kwakwalwa don tabbatar da cewa yana cikin hayyacin sa.
“Abin bakin ciki ne mutum musulmi ya yi amfani da bakinsa wajen lasar al’aurar akuya, ba tare da la’akari da koyarwar addini da kyawawan dabi’u ba,” in ji shi.
A cewar Sheikh Aminuddeen wanda ake zargin bai san komai ba game da addinin musulunci duk da kasancewarsa musulmi.
Ya ce hukumar Hisbah ba za ta saurarawa duk wadanda suke sabawa koyarwar addinin musulunci da sunan neman daukaka ba.