Jami’an tsaron ‘yan sanda da Hadin gwiwar Wasu kawarrarun Jami’an tsaro a jihar Zamfara sun kama Wata Mai Suna Fatima Lauwali bisa zargin tana safarar Makamai ga Yan Bindiga a Jihar.
Ana zarginta da bayar da makamai da alburusai ga ‘yan bindiga a jihohin Zamfara, Sokoto, Kebbi, Kaduna, Katsina, da Neja.
Kwamishinan ‘yan sandan Jihar, Ayuba Elkana, wanda ya yi holin wadda ake zargin a Gusau a ranar Juma’a, ya ce an kama Fatima mai shekaru 30 a unguwar Gada Biyu da ke karamar hukumar Bungudu, dauke da harsashi guda 991 na AK47 a hannunta, inda ta ce ta na jigilar su ne daga Dabagi Wani Kauye a jihar Sokoto ga wani da ake zargin Dan Bindiga ne mai suna Ado Alero.
A cewar kwamishinan, ta tabbatar da aikata laifin.
CP Elkana, da Tactical Operatives, da kuma hukumar FBI daga hedikwatar rundunar, karkashin jagorancin DSP Hussaini Gimba, sun kuma kama wani Babuga Abubakar bisa zarginsa da laifin taimakawa shugaban ‘yan bindiga, Lawali Na’eka, a karamar hukumar Maradun.
A Gusau, Babuga, Lawali, da Almeriya sun yi awon gaba da shanu 240, a cewar jagoran ‘yan sandan.
Sauran wadanda ake zargin kuma an kama ne bisa yunkurin fyade ga wata karamar yarinya, yunƙurin kisan kai, fashi, da kuma taimakawa ‘yan fashi.