Kotu a Amurka ta umurci FBI da hukumomin yaƙi da ƙwayoyi su saki bayanan bincike kan Tinubu

Date:

 

Kotun Ƙoli ta Ƙasa ta Washington D.C. a Amurka ta umurci manyan hukumomin tsaron kasar da su fitar da bayanan sirri da suka tattara kan Shugaban Najeriya Bola Tinubu, dangane da wani bincike da ake zargin an gudanar da shi a shekarun 1990.

Premium Times ta rawaito cewa Alƙali Beryl Howell ne ya bayar da wannan umarni a ranar Talata, yana mai cewa hana fitar da irin wannan bayani ga jama’a ba shi da ma’ana kuma ba abin yarda ba ne.

FB IMG 1744283415267
Talla

Wani ɗan ƙasar Amurka, Aaron Greenspan, ne ya shigar da ƙara a watan Yuni 2023 ƙarƙashin dokar ‘Freedom of Information Act’ (FOIA) yana ƙalubalantar ofishin Lauyoyin gwamnatin Amurka, Ma’aikatar Harkokin Waje, FBI, IRS, hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi (DEA), da kuma hukumar leƙen asiri ta CIA.

Babu ja da baya kan dokokin kare kimar addinin musulunci, Gwamnatin Kano ta fadawa kotun ECOWAS

A ƙarar da ya shigar, Greenspan ya zargi waɗannan hukumomi da karya dokar FOIA ta hanyar ƙin sakin wasu takardu da suka shafi binciken da ake zargin an gudanar kan Shugaba Tinubu da wani mai suna Abiodun Agbele.

Daga 2022 zuwa 2023, Greenspan ya shigar da buƙatun bayanai 12 zuwa hukumomi shida na Amurka, yana neman bayanai dangane da wani bincike haɗin gwiwa da FBI, IRS, DEA da ofisoshin lauyoyi na gwamnatin tarayya a arewacin Indiana da arewacin Illinois suka gudanar.

InShot 20250309 102403344

Greenspan ya ce takardun da yake nema sun shafi yanke hukunci kan ayyukan da suka haɗa da safarar kuɗi daga haramtattun kwayoyi a birnin Chicago a farkon shekarun 1990s.

A kowanne buƙatun FOIA, ya nemi bayanai kan wasu mutane huɗu da ake zargin suna da alaƙa da wannan ƙungiyar miyagun ƙwayoyi: Bola Ahmed Tinubu, Lee Andrew Edwards, Mueez Abegboyega Akande, da Abiodun Agbele.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rikicin gida: Jam’iyyar APC ta Fara Tuhumar Kakakinta na Kano Ahmad S Aruwa

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa   Jam'iyyar APC ta Mazabar Daurawa a...

Iftila’i: An Sami Ambaliyar Ruwa a garin Maiguduri

Mazauna wasu yankuna a Maiduguri, babban birnin jihar Borno...

Shugabanni ku rika gudanar da aiyukan da za su rage talauci a cikin al’umma – SKY

Daga Kamal Yakubu Ali   Fitaccen dan kasuwa a Kano Alhaji...

Muna da yakinin APC za ta lashe zabuka a Kano da Arewa don Tinubu ya yi tazarci a 2027 – Alfindiki

Jigo a jam’iyyar APCn Kano, Comrade Faizu Alfindiki, ya...