Dakarun Hisba sun kama wasu matasa yayin da su ke tsaka da wasan katin ‘Whot’
A wata taƙaitacciyar sanarwa da ta wallafa a sahfinta na facebook, rundunar ta ce jami’an ta na Ƙaramar Hukumar Warawa ne su ka kama matasan su na cikin yin wasan katin ‘Whot’ ɗin.
Daily Nigeria ta rawaito Sanarwar ta ce rundunar, a ƙarƙashin jagorancin Babban Kwamanda, Dakta Muhammad Haroon Ibn Sina, ta kama matasan ne sakamakon su na ɓata lokacinsu, maimakon su yi wani abu mai amfani.
Sanarwar ta ƙara da cewa bayan dakarun sun kama matasan, sai su ka rarraba musu wani sashe na ƙur’ani mai tsarki domin su yi taƙara.