Daga Rahama Umar Kwaru
Mataimakin shugaban majalisar dattawan Nigeria Sanata Barau Jibrin ya yabawa shugaban kasa Bola Tinubu bisa yadda ya amince da Sauya sunan Kwalejin Horas da malamai ta gwamnatin tarayya dake kano zuwa sunan Maitama sule
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai baiwa Sanata Barau Jibrin shawara kan harkokin yada labarai.
Ya ce “Saƙon Godiya ta musamman ga maigirma shugaban ƙasa bisa amincewa da buƙatar mu na canza sunan jami’ar ilimi ta tarayya dake Kano domin karramawa ga dattijon ƙasa Marigari Yusuf Maitama Sule.

“Ina mai mika godiyarmu ga mai girma shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu GCFR bisa amincewa da bukatar ɗaukacin al’ummar jihar Kano ta hannuna domin canza sunan jami’ar ilimi ta tarayya Kano zuwa jami’ar ilimi ta Yusuf Maitama Sule a Kano”.
A cikin wata sanarwar manema labarai da fadar shugaban ƙasa ta fitar ɗauke da sa hannun mai ba shi shawara na musamman kan harkokin yada labarai, Bayo Onanuga, ya sanar da sauya sunan babbar jami’ar zuwa sunan marigayi Yusuf Maitama Sule, ɗaya daga cikin manyan ‘yan siyasa daga yankin arewacin kasar nan.
Maitama Sule, Danmasanin Kano, ya kasance jami’in diflomasiyya, dan siyasa, kuma dattijon ƙasa wanda ya rasu a shekarar 2017 yana da shekara 88. Ya bayar da gudunmawa sosai ga ci gaban zamantakewa da siyasar ƙasar nan.
Yadda falakin Shinkafi ya sha ruwa da raba kayan sallah ga marayun da yake kula da su a Kano
A watan Nuwamban shekarar da ta gabata ne gwamnatin jihar Kano mai ci ta sauya sunan jami’ar Yusuf Maitama Sule da ke Kano zuwa tsohon sunan ta na Jami’ar Arewa maso Yamma ta Kano wato North West University, Kano.
Tsohin Gwamnan Kano Dakta Abdullahi Ganduje, a lokacin da yake gwamnan jihar Kano, ya sauyawa jami’ar Northwest (mallakar jihar) suna zuwa jami’ar Yusuf Maitama Sule somin tanawa da gudunmawar marigayi Maitama Sule.
Matakin da gwamnatin jihar Kano karkashin jam’iyyar NNPP ta dauka na sauya sunan jami’ar mallakar gwamnatin jihar ya haifar da ce-ce-ku-ce a jihar. Don haka na dauki nauyin gabatar da kudirin neman canza sunan Jami’ar Ilimi ta Tarayya da ke Kano zuwa sunan marigayi Danmasanin Kano.
Kamar yadda shugaban kasar ya bayyana, tunawa da gudunmawar Dan masanin Kano zai ƙara zaburar da matasanmu wajen tabbatar da gaskiya, kishin ƙasa da halayya ta gari da ya tsaya tsayin daka ya yi a lokacin rayuwarsa.
Nimet ta bayyana jihohin da za su fuskanci tsananin zafi
Marigayi Maitama Sule ya taɓa riƙe muƙamin babban wakilin Najeriya a Majalisar Ɗinkin Duniya a birnin New York, inda ya kasance shugaban kwamitin na musamman na Majalisar Dinkin Duniya kan yaƙi da wariyar launin fata.
Ya kuma taba zama Bulaliya a Majalisar Wakilai ta Tarayya tsakanin shekarar 1954 zuwa 1959, kuma ya taba zama shugaban Tawagar Najeriya yayin Zuwa Taron Kasashe Masu yancin Kan su a shekara ta (1960), haka kuma ya taɓa zama Kwamishinan hukumar karɓar Ƙorafe-ƙorafen Jama’a a Tarayya ta Farko a shekarar 1976, sannan ya taɓa zama Ministan Ma’adinai da Makamashi na Najeriya.