Daga Sani Idris maiwaya
An bukaci Hukumar Zakka da Hubusi ta jihar Kano da su fadada ayyukansu ta yadda za’a tallafawa al’umma wajen ba da Zakka yadda ya Kamata.
Mai Martaba Sarkin Kano na 16 Khalifa Muhammadu Sunusi na biyu ne ya bayyana hakan yayin da ya karbi bakuncin ayarin shugabannin Hukumar Zakka da Hubusi ta jihar Kano a Fadar sa
Yana mai cewar bada Zakka na matsayin wata hanya ta sauke nauyi daga cikin rukunan Musulunci .

” Muna fatan za ku fadada aiyukan ta yadda mutane da yawa za su amfana da zakkar, dama manufar zakka ita ce kawarwa ko rage talauci a cikin al’umma”.
Sarki Sanusi II ya yi alkawarin yin duk mai yiwuwa don baiwa hukumar zakkar dukkanin wasu shawarwari da hadin kai da goyon baya don inganta aiyukansu.
A Jawabin Sa tun da Farko, Shugaban Hukumar zakka da hubusin Barista Habibu Dan Almajir ya ce sun kai ziyara fadar Sarkin ne don neman goyon bayan Masarautar Kano bisa irin ayyukan hukumar.
Nimet ta bayyana jihohin da za su fuskanci tsananin zafi
” Mun zo wannan fadar ne don neman shawarwari da goyon bayan mai martaba ta yadda za mu inganta aiyukan wannan hukumar.
Wakilinmu ya bamu labarin cewar Shugaban Hukumar Barista Habibu Dan Almajir ya Kuma yabawa Masarautar Kano bisa irin Tarbar da akayi Musu.
Shugaban hukumar zakka da hubsin Barr. Habib Dan Almajiri ya ziyarci Sarkin tare da Commissioner l Malan Nafi’u! Umar Harazumi Da Commissioner II Malan Ali Mustapha Kuraysh da Members tare Da Daraktocin hukumar.