Daga Abdullahi Shu’aibu Hayewa
Falakin Shinkafi Amb Yunusa Yusuf Hamza, a jiya litinin ya ya yi bude baki tare da raba kayan sallah ga marayun da yake kula da su.
Idan za a iya tunawa Kadaura24 ta rawaito cewa a shekarar da ta gabata ma sai da Falakin Shinkafi ya sha ruwa da wadanan marayunasa.
Marayun maza da mata sun haura 20, kuma sun fito ne daga unguwar Yakasai dake karamar hukumar birnin Kano.

Bayan kammala Shan ruwan ne aka bi kowanne su da kayan sallah domin su na su gudanar da bikin Sallah cikin farin ciki da annushuwa.
Ya ce ya shirya musu shan ruwa ne domin ya sanya ya sanya farin ciki a zukatansu, kasancewar iyayensu Maza duk sun koma ga Allah.
Jaafar Jaafar ya fallasa sunan mai kitsawa gwamnatin Kano makarkashiya a Abuja
” Yadda ko wadanne ya’ya su ke jin dadi idan azumi ya zo, su zo su zauna da mahaifinsu suna cin abinchi, haka ni ma na zauna da wadannan yaran muka sha ruwa kuma na ga farin ciki a fuskokinsi duk, Alhamdulillah haka na ke so”. Inji falakin Shinkafi
Falakin Shinkafi ya kuma yi kira ga sauran masu hali da su rika kula da marayun kusa da su, kuma hakan zai inganta tarbiyyarsu ya kuma gyarawa mutum lahirarsa.