Daga Maryam Khamis Diso
A kokarinsa na inganta harkokin tsaro a Karamar Hukumar Birni da kewaye Shugaban Karamar Hukumar Kwamaret Fa’izu Alfindiki ya baiwa Hukumomi tsaro da yan Sintiti Motoci da Babura da kudade domin Kara inganta tsaron rayuka da dukiyoyin al’ummar yankin.
Kadaura24 ta rawaito A Jawabinsa Yayin taro Fa’izu Alfindiki yace ya rabawa Motoci da baburan ne domin dafawa kokarin Gwamnan Jihar Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje na inganta tsaron a Jihar Kano.
Ganduje ya baiwa Waɗanda Gobarar Kasuwar Kurmi ta Shafa tallafin Naira Miliyan 2
Yace Gwamna Ganduje ya tsaya tsayin daka Wajen inganta harkokin tsaro, Wanda hakan tasa jihar Kano ta zamo jiha Mafi Zaman lafiya a fadin tarayyar Kasar nan.
“ Mun raba Waɗanan Kayan ne domin tallafawa kokarin Gwamnatin Kano dana Hukumomin tsaro don inganta tsaro domin al’ummar mu su Cigaba da yin bacci da Ido biyu.” Fa’izu Alfindiki
Shugaban Karamar Hukumar ta Birni da kewaye ya bukaci Hukumomin tsaron dasu yi Amfani da Kayan da aka basu ta Hanyar data dace domin al’umma su amfana da Motoci da baburan.
Shugaban ya baiwa ‘yan Vigilante Group da Mota Kirar Ford Galaxy, ‘Yan Sanda, Civil Defence Corps da kuma DSS duk sun rabauta da sabbin mashina kirar Hero guda goma (10) duk domin inganta tsaro a fadin karamar hukumar Birni da kewayen .
Dagatai masu unguwanni da shuwagabanin kasuwa suma sun rabauta da kyautar kudi Jimilla Dubu Dari Biyar N500K.
Haka zakika, shugaban karamar hukumar ya yi alkawarin zai riga biyan kudin mai wato (Petroleum) naira dubu dari dari a duk karshen wata ga dukkanin Division din da ake dasu a fadin karamar hukumar.
A jawabinsu daban-daban, Rikunonin jami’an tsaron sun nuna farin cikinsu kuma sun bashi tabbacin cewar za suyi aiki dasu kamar yadda ya kamata domin inganta harkokin tsaro a fadin Karamar Hukumar dama Jihar Kano baki daya.