Daga Abdullahi Shu’aibu Hayewa
Shugaban majalisar limaman masallatan juma’a ta jihar Kano Sheikh Muhammad Nasir Adam ya bakaci limaman masallatan juma’a da su himmatu wajen sanar da al’ummar Musulmi illolin da kidan gwaro da tashe suke haifarwa.
” Ya kamata limamai su tunasar da al’umma cewa tashe ko kidan gwauro ba musulunci ba ne duk da ana yin sa ne a a cikin watan Ramadana, kuma yana jawo matsaloli da yawa a cikin al’umma don haka hakura da shi ya fi fa’ida”.
Sheikh Muhammad Nasir Adam ya bayyana hakan ne lokacin da yake wata ganawa ta musamman da jaridar Kadaura24.

” Ina kira ga yan uwana limaman masallatan juma’a da mu shirya tsawatar da matasa wadanda suke harkar tashe daga ranar 10 ga watan Ramadana, mun sani al’adar bahaushe ce yin tashe, a shekarun baya wannan al’ada tana nishadantar da masu yin azumi, amma a yanzu al’adar tashe tana rikidewa zuwa tashin hankali don haka ya kamata a fadakar da matasa su guji yin tashen”. Inji Sheikh Muhammad Nasir
Ya ce a yan wadannan shekarun batagari suna shiga cikin masu tashe domin tashin hankalin mutane, kuma hakan ya sabawa addinin musulunci domin ana amfani da al’adar wajen ta da hankulan jama’a.
Fyade: Kotu ta yankewa wasu mutane 3 hukuncin kisa da yanke musu Mazakuta
Sheikh Muhammad Nasir Adam ya bukaci jami’an tsaro da su yi duk mai yiwuwa don ganin an daina samun tashin hankali , koma a hana tashen baki daya don al’ummar jihar Kano su sami zaman lafiya.
Da yake nasa jawabin mataimakin kwamandan hukumar Hisbah ta jihar Kano Sheikh Dr. Muhajihid Aminudden ya ce hukumar ba zata zuba idanu a rika aikata abubuwan da suka sabawa addinin musulunci ba, musamman a wannan wata na Ramadana.
Ya ce tun da azumi ya zo hukumar ta ke aiki ba dare ba rana don ganin al’umma suna gudanar da abubuwan da suka dace a Wannan wata na Ramadana.
Dr. Mujahid Aminudden ya kuma yi kira ga iyaye da su tabbatar ya’yansu ba su shiga cikin masu kidan gwauro ko tashe ba , domin hakan a yanzu yana rikidewa zuwa tashin hankali.