Falakin Shinkafi Amb. Dr. Yunusa Yusuf Hamza ya yi kira ga shahararren dan kasuwa kuma attajirin Nahiyar Africa Alhaji Aiko Dangote da ya taimaka ya karya farashin takin zamani kamar yadda ya yiwa man fetur a Nigeria.
“Kamar yadda kowa ya sani dalilai uku ne su ka sanya aka sami hauhawar farashin takin zamani a Nigeria, na daya tsadar danyen mai a kasuwannin duniya, sai karewar darajar Naira akan Dala, da kuma kudin sufuru, kuma dukkan wadannan an sami sauki akansu don haka akwai bukatar takin shi ma ya sauka”.

Falakin Shinkafi ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da ya yi da jaridar Kadaura24.
Ya ce yadda farashin kayan abinchi ya karye a bana, akwai bukatar takin zamani shi ma ya yi sauki don manoma su sami damar yin noma a dumina mai zuwa.
An sake samu tsaiko a shari’ar neman a hana kananan hukumomin Kano kudadensu
“Mun ji manoma suna ta kukawa da karyewar farashin kayan abinchi, kuma suna kuka cewa taki har yanzu bai sauka ba, wanda suka ce hakan babbar barazana ce a gare su”. Inji Falaki
Amb. Yunusa Yusuf Hamza ya ce tabbas idan Alhaji Aliko Dangote ya taimaka aka sami saukin farashin takin zamani, to akwai yiwuwar farashin kayan abinchi su cigaba da sauka, wanda kuma hakan zai taimakawa talakawa sosai.
Ya ce kowa ya ga irin rawar da Dangote ya taka wajen rage farashin man fetur a Nigeria, kuma muddin ya taimaka haka za a sami sauki a bangaren takin zamani a kasar.