Mu na bajakolin kayan masarufi ne don saukakawa al’ummar Kano – Shugaban Gamayyar Yankasuwa

Date:

Gamayyar kungiyoyi ‘Yankasuwa ta jihar Kano sun jaddada Kudirinsu na ganin kayiyyakin masarufi sun cigaba da sauki a lungu da nako na jihar.

Shugaban kungiyoyin Barista Janaidu Zakari ne ya jaddada hakan a lokacin da yake Zantawa da jaridar Kadaura24 a filin Bajakolin da ya kasuwar ke gudanarwa a Kano.

InShot 20250115 195118875
Talla

Ya ce Kwamishinan Kasuwanci da masana’antu na jihar Kano Alhaji Shehu Wada Sagagi ya ziyarci gurin da ake gudanar da Bajakolin Kayayyakin Masarufin inda kuma ya yaba da yadda Bajakolin ke gudana, wanda ya ce ya taimaka wajen saka sakko da kayan gabanin shigowar Azimin Watan Ramadana.

Barista Janaidu Zakari ya ce an shirya bikin Bajakolin kayan masarufin ne domin kara samar da sauki ga al’ummar jihar Kano duba da halin da aka tsinci kai a ciki na matsin rayuwa.

Da dumi-dumi: An kama wani shugaban karamar hukuma a Kano

“Wannan Shiri ne na hadin gwiwa tsakanin gwamnatin Kano da manyan Yankasuwa dake fadin jihar daga Kasuwanni daban-daban domin ba da gudunmawarsu Saboda samun Falalar dake Watan Azimin Ramadana, inda yace za a ci gaba da gudanar da bajakolin kayiyyakin har zuwa 15 ga watan Ramadana Wanda watakila ma a kara wasu Kwanaki domin al’ummar jihar Kano su samu wannan Tagomashi”. Inji Barr. Junaidu Zakari

A jawabinsa tun da Farko Kwamishinan Kasuwanci ciniki da Masana’antu na jihar Kano Alhaji Shehu Wada Sagagi ya ce, sakamakon ba da gudunmawa da kungiyar SIMDA ta ke yi na tallafawa al’ummar jihar Kano, yasa gwamnati ta ga dacewar ta shigo Cikin Shirin domin ba da ta ta gudunmawar ta hanyar kafa Kwamati bisa sahalewar gwamnan Kano Alh Abba Kabir Yusuf don saukakawa al’ummar jihar da rage yawan tashin kayan Masarufi.

Kwamishinan ya ce Gwamnatin Kano da Ma’aikatar Kasuwanci ba za gajiya ba wajen taimakawa jama’ar Kano da farfado tattalin arzikin Kano da Kasa baki daya.

Haka Zalika Sagagi ya Shawarci manya da kananan ‘Yankasuwar Kano da su yi amfani da wannan lokaci na Azimin Ramadana wajen daina tashin farashin kayan masarufi. Ya Kuma bukaci Masu hali da su rika taimakawa makwotansu marasa karfi don su samu abin bude baki da na sahur.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Iftila’i: An Sami Ambaliyar Ruwa a garin Maiguduri

Mazauna wasu yankuna a Maiduguri, babban birnin jihar Borno...

Shugabanni ku rika gudanar da aiyukan da za su rage talauci a cikin al’umma – SKY

Daga Kamal Yakubu Ali   Fitaccen dan kasuwa a Kano Alhaji...

Muna da yakinin APC za ta lashe zabuka a Kano da Arewa don Tinubu ya yi tazarci a 2027 – Alfindiki

Jigo a jam’iyyar APCn Kano, Comrade Faizu Alfindiki, ya...

Bai dace ɗalibai su rika murnar kammala karatu ta hanyoyin da ba su dace ba – Mal Ibrahim Khalil

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa ‎ ‎ ‎Shugaban majalisar Malamai ta jihar Kano...