Daga Isa Ahmad Getso
Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya dakatar da mai rikon mukamin shugaban ma’aikata kuma babban sakatare na Establishment Salisu Mustapha, bisa zargin zarge-zargen da ake yi na yanke albashin ma’aikatan gwamnatin Kano.
A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa ya aikowa Kadaura24 a ranar Alhamis, ya tabbatar da cewa an kuma umurci Salisu Mustapha da ya ajiye mukaminsa na babban Sakatare na Establishment, a karkashin ofishin shugaban ma’aikata, don ba da damar gudanar da bincike ba tare da tangarda ba.

Domin tabbatar da ci gaba da gudanar da harkokin mulki, gwamnan ya amince da nadin Malam Umar Muhammad Jalo, Babban Sakatare na REPA, a matsayin sabon shugaban ma’aikata na riko, har sai an kammala binciken da ake yi.
Gwamna Yusuf ya sake jaddada matsayinsa na kin amincewa da almundahanar kudi, yana mai gargadin cewa duk wanda aka samu da laifi zai fuskanci mummunan hukunci.
Gwamnatin Kano ta bukaci Tinubu ya dauke Aminu Ado Bayero daga jihar
Kwamitin binciken da Abdulkadir Abdussalam ke jagoranta da aka kaddamar a yau, an ba shi wa’adin kwanaki bakwai don gano inda matsalar ta ke tare da gabatar da sakamakon binciken.
A farkon wannan watan ne aka nada Salisu Mustapha a matsayin shugaban ma’aikata na riko, biyo bayan hutun jinya da aka baiwa babban shugaban ma’aikatan, Abdullahi Musa, wanda yanzu haka yake jinya a kasar Indiya.