Gwamnatin jihar kano ta bukaci shugaban kasa Bola Tinubu da ya dauke sarkin kano na 15 Alhaji Aminu Ado Bayero daga jihar kano domin samar da masalaha a jihar, la’akari da yadda wasu ke amfani dawannan damar wajen neman tayar da husuma a fadin jihar .
Mataimakin gwamnan jihar kano kwamrat Aminu Abdussalam Gwarzo ne ya bayyana hakan, inda yace zaunar da sarkin kano na 15 a gidan sarkin na Nassarawa anyi shi da wata niya domin hana gwamnatin kano ta zauna lafiya da kuma kin yiwa al’ummar jihar abin da ya dace.

Freedom Radio ta rawaito kwamrat Aminu Abdussalam Gwarzo yace zanga-zanga da al’umma su ka fito a wannan satin, al’umma suna da hakkin fitowa domin nuna goyon bayan su kan abin da suke so.
Haka kuma suna da damar su nemi a cire sarkin kano na sha biyar daga gidan Nasarawa amma aka turo jami’an tsaro suka hana su tare da kama wasu daga cikinsu.
Gwamnan Kano ya kafa kwamiti domin bincikar dalilin yankewa ma’aikatan albashin
Gwarzo ya kuma ce suna kira ga shugaban kasa da ya gaggauta dauke sarkin kano na sha biyar daga cikin jihar Kano domin barin al’umma su zauna lafiya.
Gwamnatin kano ta ce yadda doka ta kawo tsohon sarkin haka doka ce ta kawo sabon sarkin dan haka abar doka ta yi aiki.