Dalilinmu na rufe wasu hanyoyi a Kano – Rundunar yansanda

Date:

Daga Rahama Umar Kwaru

 

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta bayyana cewa ta rufe wasu hanyoyin ne da suke dangana mutane da gidan sarki na Nasarawa dake kan titin zuwa gidan gwamnati saboda bayanan sirri da suka samu na kokarin kawo hargitsi a jihar.

“Mun sami bayanan sirri dake tabbatar da cewa wasu mutane na son yin zanga-zangar da za ta iya rikidewa zuwa tashin hanki, hakan ta sa rundunar ‘yan sandan tare da hadin gwiwar wasu hukumomin tsaro suka baza jami’ansu zuwa wasu muhimman wurare a cikin birnin Kano domin hana zanga-zangar da kuma tabbatar da tsaron jama’a”.

InShot 20250115 195118875
Talla

 

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na Rundunar yan sandan jihar Kano SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya aikowa Kadaura24 ranar laraba.

Ya ce “A sakamakon wadannan matakan da aka dauka, an kama wasu mutane 17 da ake zargi da aikata laifuka, kuma ana ci gaba da bincike. Rundunar zata tabbatar ta gurfanar da wadanda ake zargi da aikata wannan tashin hankali a gaban kuliya.

Fargaba: An tsaurara tsaro a Gidan Sarki na Nasarawa inda Aminu Ado Bayero ke zaune

Rundunar ta gargadin daidaikun mutane da kungiyoyi game da yin duk wani nau’i na taro, jerin gwano, bisa ka’ida ba. Kaucewa Wannan gargadi zai iya sawa jami’an tsaro su dauki mataki.

Kiyawa ya yi kira ga jama’a da su sanya ido tare da kai rahoto ga jami’an tsaro na duk wani abu da ba su aminta da shi ba, haka kuma Rundunar ta yaba da hadin kai da goyon bayan mutanen jihar Kano ke ba ta a kokarinsu na wanzar da zaman lafiya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Fadar shugaban ƙasa ta mayar da martani ga Kalaman Kwankwaso

Fadar Shugaban Ƙasa ta musanta zargin Sanata Rabiu Musa...

Yadda Kwamishina a gwamnatin Kano ya tsayawa wani dilan ƙwaya aka bada belin sa a kotu

  Kwamishinan Sufuri na Jihar Kano, Ibrahim Namadi, ya tsaya...

Kwankwaso ya caccaki gwamnatin Tinubu

  Tsohon gwamnan jihar Kano, Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso ya...

Yanzu-yanzu: Jam’iyyar APC ta yi Sabon Shugabanta na Kasa

  Ministan Jinkai da ba da Agajin Gaggawa, Farfesa Nentawe...