Da dumi-dumi: Ma’aikatan hukumar samar da ruwa ta Kano sun tsunduma yajin aiki

Date:

Daga Rahama Umar Kwaru

 

Ma’aikatan hukumar samar da ruwan sha ta jihar Kano sun tsunduma yajin aiki sakamakon wasu dalilai.

Majiyar Kadaura24 ta Hikima Radio ta rawaito Kafin su tsunduma yajin aikin sai da ma’aikatan suka yi sallah tare da gudanar da alqunuti don Allah kawo musu dauki sakamakon mawuyacin halin da suke ciki.

Sun dai bayyana cewa sun tsunduma yajin aikin ne sakamakon yadda gwamnati ta Kasa fara biyansu mafi karancin albashi na naira 71,000 da gwamnan Kano ya Amince da shi.

InShot 20250115 195118875
Talla

Sun kuma ce bayan kin biyansu mafi karancin albashin, sun akwai ragowar hakkokinsu da suka ce gwamnatin Kano ta gagara biyansu.

Majalisar Limaman Masallatan Juma’a ta bayyana goyon bayanta ga matakin gwamnatin na tantance Kungiyoyin farar hula

Dukkanin kokarin da muka yi na jin ta bakin Manajan Daraktan hukumar samar da ruwan sha ta jihar Kano don jin na su bahasin ya ci tura, Amma za mu cigaba da bibiyar lamarin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamnatin Kano za ta fara jiyo ra’ayoyin al’umma kafin gudanar da duk wani aiki a jihar – Bilkisu Indabo

Daga Samira Hassan   Gwamnatin jihar Kano ta sha alwashin nan...

Kwankwaso ya gana da Tinubu a fadar shugaban kasa

Daga Nasiba Rabi'u Yusuf   Tsohon gwamnan jihar Kano, Rabiu Kwankwaso,...

Neman Ilimin addini dana boko da sana’a ba kishiyoyin juna ba ne – Dr. Aminu Sagagi ga matasan Zango

Daga Rahama Umar Kwaru   Wani Malamin addinin musulunci a kano...