An sace wata mata mai shekaru 65 a wani asibitin a Kano

Date:

Wasu da ake zargin masu garkuwa da Mutane ne sun sace wata mata mai shekaru 60, Talatu Ali, daga Asibitin masu larurar kwakwalwa da ke Dawanau a karamar hukumar Dawakin Tofa, Jihar Kano.

Rahotanni sun bayyana cewa lamarin ya faru ne a lokacin da take jiran ganawa da likita.

InShot 20250115 195118875
Talla

Daily Trust ta rawaito cewar masani kan yaki da ta’addanci, Zagazola Makama, ɗan uwanta Nasiru Aliyu tare da wani ɗan uwanta, Aliyu Garba, ne suka kawo ta asibitin a ranar 19 ga Fabrairu, 2025.

Amma yayin da suke layin jiran ganawa da likita, sai suka lura cewa ba su iya gano inda take ba.

 

Duk ƙoƙarin da aka yi don gano ta a cikin harabar asibitin ya ci tura, lamarin da ya sa iyalanta suka kai rahoto ofishin ‘yansanda na Dawanau.

Rikicin APC: Abdullahi Abbas ya mayarwa da Minista Abdullahi Ata Martani

Sai dai, a ranar 21 ga Fabrairu, 2025, da misalin ƙarfe 7:00 na safe, Aliyu ya samu kiran waya daga wani lamba da ba a sani ba inda aka tabbatar masa cewa matar tana hannunsu.

Rundunar ‘yansandan Jihar Kano ta tabbatar da faruwar lamarin.

Ko da yake yankin Arewa maso Yamma na fama da matsalolin ‘yan fashi da garkuwa da mutane, Kano ta kasance cikin yanayi na zaman lafiya a mafi yawan lokaci.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Bai dace ɗalibai su rika murnar kammala karatu ta hanyoyin da ba su dace ba – Mal Ibrahim Khalil

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa ‎ ‎ ‎Shugaban majalisar Malamai ta jihar Kano...

Budaddiyar Wasika ga Gwamnan Kano kan wanda zai maye gurbin Muhuyi Magaji R/gado daga Kungiyar Lauyoyi yan Kano

Zuwa ga Mai Girma Alhaji Abba Kabir Yusuf Gwamnan Jihar Kano Gidan...

Dan majalisa Bichi ya sake biyan kuɗin makarantar dalibai 121 masu karatun digiri na biyu da na digirin digirgir

Ɗan Majalisar Wakilai mai wakiltar Mazabar Bichi a Majalisar...