An sace wata mata mai shekaru 65 a wani asibitin a Kano

Date:

Wasu da ake zargin masu garkuwa da Mutane ne sun sace wata mata mai shekaru 60, Talatu Ali, daga Asibitin masu larurar kwakwalwa da ke Dawanau a karamar hukumar Dawakin Tofa, Jihar Kano.

Rahotanni sun bayyana cewa lamarin ya faru ne a lokacin da take jiran ganawa da likita.

InShot 20250115 195118875
Talla

Daily Trust ta rawaito cewar masani kan yaki da ta’addanci, Zagazola Makama, Ι—an uwanta Nasiru Aliyu tare da wani Ι—an uwanta, Aliyu Garba, ne suka kawo ta asibitin a ranar 19 ga Fabrairu, 2025.

Amma yayin da suke layin jiran ganawa da likita, sai suka lura cewa ba su iya gano inda take ba.

 

Duk Ζ™oΖ™arin da aka yi don gano ta a cikin harabar asibitin ya ci tura, lamarin da ya sa iyalanta suka kai rahoto ofishin ‘yansanda na Dawanau.

Rikicin APC: Abdullahi Abbas ya mayarwa da Minista Abdullahi Ata Martani

Sai dai, a ranar 21 ga Fabrairu, 2025, da misalin Ζ™arfe 7:00 na safe, Aliyu ya samu kiran waya daga wani lamba da ba a sani ba inda aka tabbatar masa cewa matar tana hannunsu.

Rundunar ‘yansandan Jihar Kano ta tabbatar da faruwar lamarin.

Ko da yake yankin Arewa maso Yamma na fama da matsalolin ‘yan fashi da garkuwa da mutane, Kano ta kasance cikin yanayi na zaman lafiya a mafi yawan lokaci.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related