Za mu kashe Sama da Naira miliyan 105. Dan Bunkasa Harkar ilimi a karamar hukumar Dala – Hon Surajo Imam

Date:

Daga Sani Idris maiwaya

 

Shugaban karamar hukumar Dala Alhaji Surajo Imam ya bayyana Mahimmancin Malamai a cikin al’umma da cewar wata hanya ce da ka iya ciyar da Rayuwar al’umma Gaba .

Shugaban karamar hukumar Dala Alhaji Surajo Ibrahim Imam shi ne ya bayyana hakan yayin da ya Karbi bakuncin Kungiyar Malaman Makaranta ( NUT ) Reshen Karamar hukumar Dala a ofishin sa

Shugaban karamar hukumar Dala Alhaji Surajo Ibrahim Imam ya Kara cewar tabbas Malamai na da Matukar Mahimmanci wajen samar da ilimi ga Dalibai.

InShot 20250115 195118875
Talla

Haka Kuma ya Kara da cewar Mai girma Gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf na Bawa Harkar ilimi kulawar data kamata musamman a wannan karamar hukumar ta Dala.

Inda a wannan Karon Gwamnan ya Sahalewa karamar hukumar Dala dan gyara Sashin Kula da ilimi na Yankin Wanda Ake sa ran za’a kashe Naira miliyan 105.

Yadda Gwamnan Kano ke shirin zamanantar da sana’ar fawa – Hon. Sani Rabi’u Rio

A nasa bangaren tun da farko Shugaban Kungiyar Malaman Makarantar ta ( NUT ) Malam Yahaya Ramadan ya yaba da Yadda Shugaban karamar hukumar Dala Shima ke Bawa Harkar ilimi kulawar data kamata

Malam Yahaya Ramadan ya Kuma ce wannan Kungiyar tana Mai Kara Mika godiya Ga gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf bisa karin girman Ga Malamai da Kuma Samar da Kayan Makaranta ( uniform ) Ga Dalibai.

Shi ma a nasa Jawabin Shugaban Kungiyar hedimastoci Malam yakubu Abubakar ya bayyana farin cikin sa Kan irin tarbar da suka samu daga Shugaban karamar hukumar Dala.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Yadda Manoma a Nigeria ke cigaba da kokawa saboda karyewar farashin kayan abinchi

  Farashin kayan abinci kamar masara, gero da shinkafa na...

Inganta ilimi: Jaridar New Telegraph ta Karrama Gwamnan Kano

Daga Maryam Muhammad Ibrahim   Gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir...

Sanarwa ta musamman ga masu neman shiga aikin dansanda

Hukumar kula da aikin 'yan sanda na Kasa (POLICE SERVICE...

Zaben 2027: Kwankwaso ya bugi kirji

Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, tsohon gwamnan jihar Kano, ya...