Zargin batanci: Kotu ta aikewa Abdullahi Abbas da Faizu Alfindiki sammaci

Date:

Babbar Kotun Shari’ar Musulunci da ke kasuwa, ƙarƙashin Mai Shari’a Abdu Abdullahi Waiya, ta aike da sammaci ga shugaban jam’iyyar APC na Kano, Abdullahi Abbas, da Faizu Alfindiki, ɗan APC bisa zargin yin batanci ga gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf.

Freedom Radio ta rawaito cewa, wasu hadiman gwamnan, Amir Abdullahi da Ishaq Abdul ne su ka shigar da ƙarar, inda su ke zargin Abdullahi Abbas da Faizu da batanci ga gwamnan Yusuf ta hanyar WhatsApp da facebook.

InShot 20250115 195118875
Talla

A zaman kotun na yau, lauyan masu ƙara, Shazali Muhammad Ashiru, ya shaidawa Freedom Radio cewa sun shigar da karar ne bisa kalaman da wadanda ake ƙarar ke yi.

A cewar sa, “kalaman sun yi muni kuma za su iya haifar da tunzuri daga al’ummar jihar Kano masoya gwamna da ma a halin mai girma Gwamna”.

“Don haka sai mu ka ga cewa doka ta bada damar duk wanda ya ga ana wani abu da zai iya haifar da rashin kwanciyar hankali zai iya garzayawa zuwa kotu ya shigar da kara domin wanzar da zaman lafiya.

Kwanaki 100: Shugaban karamar hukumar Wudil ya kaddamar da wasu aiyukan raya kasa

“Kalaman da Abdullahi Abbas da Faizu Alfindiki sun yi muni ga muhibbar mai girma Gwamnan Kano kuma ko waye aka fadawa haka zai iya zuwa kotu ya nemi hakkin sa,” in ji lauyan.

Kotun ta kuma sanya 24 ga watan Fabrairu domin dawowa gaban kotun.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Sabon Rikici Ya Kunno Kai Cikin Jam’iyyar APC a Kano

Daga Aliyu Danbala Gwarzo   Karamin Ministan gidajen da raya burane...

Yadda Manoma a Nigeria ke cigaba da kokawa saboda karyewar farashin kayan abinchi

  Farashin kayan abinci kamar masara, gero da shinkafa na...

Inganta ilimi: Jaridar New Telegraph ta Karrama Gwamnan Kano

Daga Maryam Muhammad Ibrahim   Gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir...

Sanarwa ta musamman ga masu neman shiga aikin dansanda

Hukumar kula da aikin 'yan sanda na Kasa (POLICE SERVICE...