Daga Aliyu Danbala Gwarzo
Zababbiyar shugabar karamar hukumar Tudun wada Hajiya Sa’adatu Salisu Yusha’u soja ta zama shugabar kungiyar Shugabannin Kananan hukumomin Kano 44 ta jihar Kano.
Kungiyar kuma ta zabi Hon. Jamilu Ɗambatta Shugaban Karamar Hukumar Dambatta a matsayin mataimakin shugabar kungiyar.

Haka zalika, an zabi Hon. Hamza Maifata shugaban Karamar hukumar Bichi a matsayin Sakataren kungiyar Shugabannin kananan hukumomin jihar Kano.
Hajiya Sa’adatu Salisu Yusha’u dai ita zata jagoranci kungiyar Shugabannin kananan hukumomin jihar Kano na tsahon shekaru 3 ma su.
Dantata ya kaddamar da cibiyar koyawa daliban Makarantar Dala Sana’o’i da kungiyar DOGAA ta gina
Tuni dai Shugabar kungiyar ta jagoranci sauran Shugabannin kungiyar, inda su ka ziyarci gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf a daren jiya asabar.
Rahotanni sun nuna cewa sun yi ganawar sirri da gwamnan, sai dai har yanzu ba’a sanar da manema labarai abun da suka tattauna ba.