Dantata ya kaddamar da cibiyar koyawa daliban Makarantar Dala Sana’o’i da kungiyar DOGAA ta gina

Date:

Daga Rukayya Abdullahi Maida

 

Kungiyar tsofaffin daliban makarantar yan mata ta Dala ( DOGAA) ta yi bikin kaddamar da cibiyar horar da daliban makarantar sana’oi da kuma Sakatariyar DOGAA.

Da ya ke bayyana makasudin samar da cibiyar Shugaban Kwamitin Amintattu na Kungiyar Alhaji Tajuddeen Aminu Dantata, ya ce kasancewar duk wanda ya koyar da mace sana’a ko ilimi tamkar ya koyar da al’umma ne wannan ta sa aka samar da cibiyar horar da yan matan sana’oi kafin su kammala karatu su sami ilimin sana’a domin dogaro da Kansu.

Da yake jawabi yayin zantawa da manema labarai uban Kungiyar Alh. (Dr) Aminu Alhassan Dantata ya ce yayi farin cikin kasancewar shi a wurin kaddamar da cibiyar da kuma Sakatariyar Kungiyar DOGAA, Mai suna Rabi Tajudeen Aminu Dantata skills Acquisition center and DOGAA Secretariat.

InShot 20250115 195118875
Talla

Sannan ya godewa yan makarantar da su ka dage wajen kaita matakin Nasara da cigaba, inda ya ce kamata ya yi dalibai suvyi koyi da tsaffin dalibai makarantar Dala, ta hanyar bibiyar makarantun da su ka yi karatu su ga halin da suke ciki don su taimaka.

Daga nan Dr. Aminu Dantata ya yi kira ga masu hannu da shuni da Shugabanni da yansiyasa da kuma masu mulki cewa su taimaki al’umma ta kowace fuska duba da yanayin da ake ciki.

Sanusi Bature da Abokansa Sun Tallafawa Wata Makarantar Islamiyya da Naira Miliyan 3 a Kano

Hon. Saudatu Sani ita ce shugabar Kungiyar ( DOGAA) ta kasa ta yi wa Allah godiya da ya nuna mata ranar sauke wannan Nauyi cewar ta.

Hon. Saudatu ta kara da cewa an tara musu kudi Sama da Naira miliyan dari da taimakon Uban Kungiyar Alh. Aminu Dantata, Wanda da wadannan kudi aka aiwatar da aikin samar da cibiyar sana’oin mai dauke da dakin koyar da gwajegwaje da kuma ajin kekunan dinki don bawa dalibai Horo.

Bangaren Sakatariyar kuwa akwai Babban dakin taro da ofisoshi dama Wurin shakatawa Duka don inganta ilimin daliban kamarantar Dala da Kungiyar DOGAA ta sanya a gaba.

Gidauniyar Da’irar ma’aiki (S A W) ta rabawa marayu da masu bukata ta musamman suturu a Kano

A Karshe ta yi godiya ga dukkanin wadanda suka bada gudunmawa Musamman Shugabannin Kungiyar na kasa da Kwamitin Amintattu, wajen ganin komai anyishi bisa Amana da kuma nasara.

Amina Muhd Nasir guda ce daga cikin dalibai makarantar GGC Dala da za su koyi dinki a sabuwar cibiyar ta Bayyana Jin dadinta bisa yadda zasu amfana dama sauran dalibai masu tasowa nan gaba da wannan horo da zasu samu.

Amina ta ce da zarar sun kammala karatu za su kasance masu dogaro da Kansu da sana’oin da za’a koya musu koda basu samu aikin Gwamnati ba.

Taron ya gudana ne a ranar Asabar a dakin taro na GGC Dala dake karamar Hukumar Dala a Jihar Kano, inda ya samu halartar manyan Baki na kusa da na nesa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Zargin Almundahana: ICPC zata gurfanar da shugaban hukumar zabe ta Kano da wasu mutum biyu

    Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta (ICPC)...

Dalilin da ya hana ni zuwa Kano tarbar Tinubu – Ganduje

Daga Rukayya Abdullahi Maida   Tsohon shugaban jam’iyyar APC na kasa,...

Shugaban RATTAWU na Kano ya taya sabbin shugabannin kungiyar na kasa murna

Daga Aliyu Danbala Gwarzo   Shugaban kungiyar ma’aikatan rediyo, Talabijin da...

Dalilina na ziyartar gwamnan Kano Abba – Inuwa Waya

Daga Rahama Umar Kwaru Tsohon Wanda ya nemi Zama Dan...