Cire Tallafin Man Fetur: Buhari yace Zai rabawa ‘yan Nigeria tallafin Naira Dubu biya-biyar

Date:

Gwamnatin Najeriya ta ce za ta raba wa ƴan Najeriya tallafin sufuri na naira 5,000 a madadin tallafin mai da za ta janye gaba ɗaya zuwa 2022.

Ministar kuɗin ƙasar Zainab Ahmed Shamsuna ce ta bayyana haka a ranar Talata a wani taron Bankin Duniya kan ci gaban Najeriya.

Buhari ya Amince a baiwa Kowacce Jiha tallafin Naira Biliyan 18

Ministar ta ce adadin waɗanda za su amfana da tallafin ya dogara ne da yawan abin da ke hannu bayan janye tallafin.

“Kafin kammala janye tallafin mai a tsakiyar 2022, muna aiki tare da abokan hulɗarmu kan matakai da suka kamata na rage tasirin janye tallafin ga talakawa.”

“Ɗaya daga cikin matakan shi ne tsarin biyan tallafin sufuri ta hanyar tura wa ƴan Najeriya tsakanin miliyan 30 zuwa 40 kuɗi,” in ji ta.

BBC Hausa ta rawaito Alƙalumman Bankin Duniya sun nuna cewa kashi 40 na talakawan Najeriya, kashi uku kawai na fetur suke amfani da shi a ƙasar, tare da nuna cewa masu arziki ne suke amfana da tallafin mai da gwamnati ke biya.

3 COMMENTS

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Nazarin Yadda Shaharar Sanata Barau Ta Karade Nigeria – Abba Anwar

Daga Abba Anwar Wani babban abin lura game da rayuwar...

Kungiyar Ɗaliban Mariri ta gudanar da aikin duba marasa Lafiya kyauta a yankin

Daga Abdallahi Shu'aibu Hayewa   Kungiyar Dalibai ta Makarantar Mariri wato...

Gwamnan Taraba ya bayyana dalilinsa na shirin komawa APC

Gwamnan jihar Taraba, Agbu Kefas, ya ce zai shiga...

Gwamna Abba Ya Sanya Hannu Kan Dokar Kafa Gaya Polytechnic

Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya sanya...