Gwamnatin jihar Neja a Nigeria ta ce zata karya farashin kayan abinchi sakamakon gabatowar watan azumin Ramadan.
Gwamnan jihar Neja, Umar Bago ya sanar da hakan ne lokacin da ya karɓi baƙuncin tawagar gidauniyar ‘Gates’ a gidan gwamnatin jihar da ke Minna.

Gwamna Bago ya ce ya ɗauki matakin ne domin sauƙaƙa wa al’umma a lokacin azumin watan Ramadan.
Idan za a iya tunawa Kadaura24 ta duk lokacin watan azumin Ramadan al’umma su kan koka da yadda yan kasuwa ke tsauwala farashin kayan masarufi saboda yadda ake yawan amfani da su.