Atiku Abubakar ya yi ganawar sirri da Obasanjo

Date:

Dan takarar shugaban ƙasa na Jam’iyar PDP a zaɓen 2023, Atiku Abubakar, ya yi wata ganawar sirri da tsohon Shugaban Ƙasa kuma tsohon uban gidansa, Olusegun Obasanjo.

Obasanjo da Atiku sun yi ganawar ne a yayin ziyarar da tawagar Atiku ta kai gidan Obasanjo da ke mahaifarsa a Jihar Ogun.

InShot 20250115 195118875
Talla

A ranar Litinin ne Atiku tare da rakiyarsa ciki har da tsohon Gwamnan Jihar Kuros Riba, Liyel Imoke, da tsohon Gwamnan Sakkwato Sanata Aminu Waziri Tambuwal da kuma Sanata Abdul Ningi mai wakiltar Bauchi ta Tsakiya.

Ku mai da hankali wajen gina rayuwar al’umma – Sarkin Kano na 16 ga Kungiyar matan Arewa

Isar tawagar Atiku da tawagarsa gidan Obasanjo ke da wuya shugabannin biyu suka sanya labule domin ganawar sirri.

Har yanzu dai ba a bayyana abubuwan da suka tattauna ba, sai dai ana ganin hakan ba zai rasa nasaba da zaben shekara ta 2027 ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Kansila a K/H Garum Mallam ya rabawa marayu 300 kayan Sallah

Daga Safiyanu Dantala Jobawa   Sama da yara mayaru 300 ne...

Sallah: Baffa Babba ya raba buhu 2,000 na Shinkafa ga Kungiyoyin Tinubu a Kano

Babban daraktan cibiyar kula da ingantuwar aiyuka ta kasa...

Babbar Sallah : Kansilan Lajawa ya raba Naira dubu 500 ga al’ummar mazabarsa

Daga Nura Adam   Kansilan mazabar Lajawa a karamar hukumar Wudil...