Jam’iyyar APC ta kori tsohon gwamnan jihar Osun kuma tsohon ministan cikin gida Rauf Aregbesola, a kan zarginsa da yin abubuwan da suka saba wa jam’iyyar.
Reshen jam’iyyar na jihar ta Osun shi ne ya tabbatar da korar a wata wasika da ya fitar.
Aregbesola, wanda ya kasance ministan cikin gida a lokacin gwamnatin da ta gabata, ya jagoranci wani bangare na jam’iyyar ta APC a jihar, bangaren da aka yi wa lakabi da “The Osun Progressives,” wanda kuma daga baya aka sake masa lakabi da ”Omoluabi Caucus”.
Babban Dalilin da ya sa na Shiga Siyasa – Sani Danja
Korar tsohon gwamnan ta biyo bayan taron da bangaren da yake jagoranta ne wato Omoluabi Caucus, ya gudanar kuma karkashin jagorancin, Aregbesola.
A lokacin taron bangaren ya sanar da aniyarsa ta ficewa daga APC,inda ya bayar da hujjar raguwar tasirin jam’iyyar a jihar.