Daga Khadija Abdullahi Aliyu
Gwamnatin jihar Kano ta yi alkawarin yakar shaye-shayen miyagun kwayoyi ta hanyar baiwa matasa ingantaccen ilimi.
Kadaura24 ta rawaito mai baiwa gwamnan jihar Kano shawara na musamman kan harkokin Matasa da wasanni Alhaji Sani Musa Danja ne ya bayyana hakan lokacin da ya ziyarci jami’ar Sheikh Isyaka Rabi’u KHAIRUN dake Kano.
“Al’amarin shaye-shayen miyagun kwayoyi da wasu daga cikin matasan mu suke yi, yana ci mana tuwo a kwarya hakan tasa muka ga dacewar mu zo domin kulla alakar da jami’ar KHAIRUN domin ganin sun cimma manufar gwamnatin mu ta samar da ilimi ga matasa”. Inji Sani Danja

” Samar da ilimi da kawar da shaye-shaye na daga cikin kudirin mai girma Gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf domin ceto yara matasa daga harkar shaye shaye da zaman kashe wando”.
Tinubu ya ba da umarnin a baiwa Kwankwaso, Bichi da sauran wadanda ya nada takardun kama aiki
” mun San Wannan jami’ar mai zaman kanta ce , amma Muna so a samar da tsarin da zai saukakawa matasa don sun sami ingantaccen ilimi don kyautata rayuwarsu.
A nasa jawabin shugaban jami’ar KHAIRUN Prof. Abdulrashid Garba bayan nuna farin cikinsa ga ziyarar mashawarcin gwamnan kan harkokin Matasa da wasanni, ya kuma ba da tabbacin jami’ar KHAIRUN zata hada kai da ofishinsa Sani Danja don inganta rayuwar matasa.