Daga Rukayya Abdullahi Maida
Gwamnatin jihar Kano ta jaddada Aniyarta na taimakawa matasa don cigaban rayuwar su ta fannoni daban-daban.
Hon. Sani Musa Danja Mai baiwa gwamna Shawara Musamman kan cigaban matasa a sha’anin wasanni ne ya bayyana haka ga manema labarai a ofishin sa.

Sani Danja ya ce dole sai an jure wurin wayar da kan matasa Musamman wadanda suka dauki gabarin shaye-shaye ko daba, har ayi nasarar cimma burin kawar musu da mummunan tunani.
“Za mu tabbatar sun ajiye waccen dabi’ar sannan mu samar musu da ilimi, yadda za su zama abin koyi kamar yadda jagoran kwankwasiyya yayi har aka cimma nasara a kwankwasiyya, kuma Gwamna shi ma ya gada”.
Maulidin Inyass: Kashim Shattima ya Jinjinawa Mabiya Darikar Tijjaniyya na Nigeria
Sani Danja ya ce yana da manufofin bunkasa rayuwar matasan jihar Kano, din haka ya ce zai yi iya kokarinsa don cimma wadancan manufofi.
Daga nan mai baiwa Gwamnan Shawara kan cigaban matasa da sha’anin wasanni Sani Danja ya ce, idan har muka bada gudunmawa kasa zata canja kuma ta gyaru musamman ta hanyar Taimakon Mutane don cigaban jihar kano.
Karshe ya ce matasa sune kashin bayan cigaban Al’umma, don haka wajibi a tsaya tsayin daka don inganta rayuwarsu, Domin idan matasan Kano suka gyaru za su zama masu kishin jihar, hakan zai sa su rika yin abubuwa masu amfani da kowacce jiha a kasarnan zata yi koyi da su.