Tsohon Kwamishinan Kananan Hukumomin na jihar Kano kuma dan takarar mataimakin Gwamna a jam’iyyar APC a zaben shekarar 2023, Murtala Sule Garo ya bayyana damuwa kan rashin jituwa da ake samu tsakanin tsoffin gwamonin jihar da suka hada da Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso da Abdullahi Umar Ganduje.
Kwankwaso da Ganduje, waɗanda abokan siyasa ne a da, sun tsunduma cikin rikicin da ya ƙi ya ƙi cinye wa ton 2016.
Sai dai a yayin da ya ke jawabi a taron tsofaffin ƴan majalisar jiha na majalisa ta 8 da ta 9 na jihar Kano, Garo ya yi kira ga Ganduje da Kwankwaso su hada kai don ciyar da Kano gaba.
“Kira na shi ne bangaren Gwamonin mu, Abin takaici a jihar Kano, ka ga jiha irin jihar Zamfara wacce ta ke kanwa ce ta nesa ga Kano , tsoffin gwamnoninsu za ka ga an yi taro dukkan su sun zo , sun hadu duk da banbancin ra’ayi da na jam’iyya ,amma duk da haka su kan hadu su tattauna abinda zai ci da jiharsu gaba”.

“Amma mu a nan jihar Kano, abin mamaki shugabannin mu, iyayenmu tsofaffin Gwamnoni ba za su iya haduwa su tattauna abinda zai kawo ci gaba ga jihar Kano ba .
“A don haka mu na rokon su, mu na kira gare su da su hade kansu mu na yi musu addu’a, lallai su kawar da banbance- banbancen da ke tsakanin su indai da gaske su na son ci gaban Kano”,inji Garo.