Dukkanin dalibai 150 da suka kammala digirinsu na 2 a India mun dauke su aiki – Gwamnan Kano

Date:

Daga Rahama Umar Kwaru

 

Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya tarbi yan asalin jihar kano 159 da gwamnatinsa ta tura su kasar India suka yo karatun digiri na biyu.

A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa ya aikowa Kadaura24, daliban sun iso filin jirgin sama na Malam Aminu Kano da misalin karfe 12:55 na ranar Asabar, inda suka samu tarba daga gwamna da mataimakinsa da sauran manyan jami’an gwamnati ciki har da kwamishinoni.

Matasan sun kimanin 150 na daga cikin Mutane 420, kashin farko na mutane 1000,1 da da gwamnatin Kano ta tura jami’o’i daban-daban na duniya domin su yo digiri na biyu .

Talla

Baya ga dalibai 150 da aka yaye daga Jami’ar Sharda, Akwai mutane 98 da aka tura Jami’ar Mewar, 58 daga Jami’ar Symbiosis, 30 daga Jami’ar Kalinga, 29 daga Jami’ar SR, 23 daga Jami’ar Swarnim, sai mutane 33 daga Jami’ar Musulunci ta Uganda (IUIU) .

Gwamna Yusuf, a wani taron liyafa da aka gudanar a gidan gwamnatin Kano, ya yabawa daliban bisa kwazon da suka nuna, inda ya bayyana cewa shirin bayar da tallafin karatu zuwa kasashen waje wani ginshiki ne na manufofin gwamnatinsa na bunkasa rayuwar dan Adam.

Dan jihar Kano ya zama zakara a gasar musabakar al’qur’ani ta Kasa

Ya jaddada rawar da shirin ke takawa wajen baiwa matasa masu hazaka damar samun cigaba a bangarori masu mahimmanci na rayuwar al’umma.

Gwamnan ya sanar da daukar daliban da suka dawo aiki kai tsaye, wadanda suka kammala karatun digirinsu na biyu a fannin injiniya, likitanci, hada magunguna, da sauran fannonin da suka shafi lafiya.

Wannan matakin ya kara jaddada kudirin gwamnatin na magance karancin kwararrun jami’an kiwon lafiya da inganta tsarin kiwon lafiya na jihar da samar da ababen more rayuwa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Zargin kisa a R/Zakara: Gwamnatin Kano za ta kafa kwamiti – Waiya

Gwamnatin jihar Kano, ta ce za ta gudanar da...

Majalisar Dokokin Kano ta yi Doka kan masu tufar da yawu da majina a titi

Majalisar Dokokin jihar Kano ta amince da dokar cin...

Sanata Barau zai baiwa dalibai 1,000 tallafin karatu a Kano ta tsakiya da ta Kudu

Daga Aliyu Danbala Gwarzo   Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau...

Kamfanin Gerawa ya ba da tallafin Kwamfutoci 100 ga al’ummar Gezawa

Daga Abdulmajid Habib Tukuntawa   Kamfanin shinkafa na Gerawa Rice Mills...