Da yammacin ranar Alhamis ne a ka fara yaɗa labarin cewa an kai mummunan hari a Babban Bankin Najeriya (CBN) musamman a dandalin sada zumunta na Facebook.
Jita-jitar ta yaɗu cewa an kai harin ƙunar baƙin wake a babban bankin inda aka tafka ɓarna mai yawa.
Har wa yau, jita-jitar ta yaɗu ne a tsakanin wasu shafuka da suke yaɗa abubuwansu da harshen Hausa waɗanda ba gidajen jaridu ba na.
Sai dai binciken da daily Trust ta gudanar ya tabbatar da cewa hotunan da ake yaɗawa na ƙarya ne, kuma an hada su ne da sabuwar basirar na’ura ta (AI).
Ga hotunan da Aka hada da sabuwar fasahar AI