Galibi shugabannin ƙasashen duniya kan yi tafiye-tafiye zuwa ƙasashen ƙetare domin tafiya ta aiki ko ta ƙashin kai.
Waɗanann tafiye-tafiye kan haɗa ta taruƙan ƙungiyoyin ƙasashe da bisa gayyatar shugaban wata ƙasa ko tafiya hutu, ko neman lafiya.
A nasa ɓangare shugaban Najeriya, Bola Tinubu, kamar sauran takwarorinsa shugabannin ƙasashen duniya, ya yi bulaguro da dama zuwa ƙasashen daban-daban a shekarar mai ƙarewa.
A wannan maƙala mun yi ƙoƙarin zaƙulo wasu daga muhimman tafiye-tafiyen da shugaban na Najeriya ya yi zuwa wasu ƙasashen waje, da dalilan yinsu, ta hanyar bibiyar sanarwar bulaguron da fadarsa ke fitarwa a duk lokacin da zai yi bulaguron.
A ranar 24 ga watan Janairun 2024, shugaban na Najeriya ya buɗe bulaguronsa na wannan shekara, bayan da ya tafi ƙasar Faransa domin ziyarar ƙashin kai.
Cikin sanarwar bulaguron da fadar shugaban ƙasar ta fitar, ta ce zai koma Najeriya a satin farko watan Fabrairu.
Sanarwar ba ta yi cikakken bayani game da bulaguron shugaban ba, to sai dai wataƙila hakan ba ya rasa nasaba da kasancewar saboda ziyarar ta kashin kai ce.
Sai kuma a ranar 14 ga watan Fabrairun shekarar, inda shugaban ya hau jirgi zuwa taron ƙungiyar ƙasashen Afirka ta AU da aka gudanar a birnin Addis Ababa, na ƙasar Ethiopia .
A taron – wanda shi ne karo na 37 da shugabannin ƙasashen Afirka ke ganawa- Shugaba Tinubu ya tattauna takwarorinsa kan yadda Afirka za ta taimaka wajen yaƙi da sauyin yanayi da kuma ƙoƙarin nahiyar na ganin ta samu wakilci na ƙungiyar G20, kamar yadda sanarwar da fadarsa ta fitar a lokacin.
Sanata Barau Ya Zo Na Ɗaya Wajen Gabatar da Mafi Yawan Ƙudurori a Majalisar Dattawa
Amsa gayyatar sarkin Qatar
A ƙarshen watan ne kuma shugaban ya shirya wata ziyarar kwanaki biyu zuwa ƙasar Qatar da ke yankin Larabawa.
Shugaba Tinubu ya kai ziyarar ne bisa gayyatar da sarkin Qatar, Sheikh Tamim bin Hamad Al Thani, ya yi masa, kamar yadda wata sanarwa daga fadarsa ta bayyana.
Sanarwar ta ƙara da cewa a lokacin ziyarar Shugaba Tinubu zai tattauna da sarkin Qatar, kan batutuwan da za su ƙarfafa haɗin kai tsakanin ƙasashen biyu cikin har da batun samar da tsaro da ci gaban tattalin arziki.
A ranar 1 ga watan Afrilun shekarar ne kuma, Shugaban na Najeriya, ya tafi zuwa Senegal domin halartar bikin rantsar da sabon shugaban ƙasar, Bassirou Faye.
Shugaba Tinubu ya halarci a bikin a lokacin bisa gayyatar da gwamnatin Senegal ta yi amsa a matsayin shugaban Ƙungiyar Raya Tattalin Arzikin Yammacin Afirka ta Ecowas.
Sai kuma a ranar 23 ga watan na Afrilu, Shugaban Tinubu ya masa gayyatar firaministan Netherlands, Mark Rutte zuwa ƙasar domin ziyarar aiki.
A lokacin da ya je ƙasar, Shugaba Tinubu ya halarci taron zuba jari da kasuwanci tsakanin ƙasashen biyu, kamar yadda yake cikin sanarwar da fadarsa ta fitar a lokacin bulaguron.
Haka kuma lokacin ziyarar shugaba Tinubu ya gana da firaministan da kuma Sarkin, ƙasar, Willem-Alexander, da sarauniya Maxima ta ƙasar.
Bayan kammala ziyarar aiki ta kwana biyu a Netherlands, Shugaba Tinubu ya zarce ƙasar Saudiyya a ranar 26 ga watan na Afrilu, domin halartar taron tattalin arziki na duniya.
Taron – wanda aka gudanar a birnin Riyadh – ya tattauna batun haɗin kan kasuwancin tsakanin ƙasashen duniya da ci gaba da samar da makamashi.
Shugabannin ƙasashe da ƙungiyoyin kasuwanci fiye 1,000, da kuma masana fiye da 90 ne suka halarci taron, kamar yadda fadarsa ta bayyana cikin sanarwar da ta fitar a lokacin.
Duk sati ana hada-hadar Naira biliyan 50 a kasuwar shanu ta Wudil – Shugaban kasuwar
‘Halartar bikin rantsarwa’
A ranar 23 ga watan Mayu ne kuma, shugaban na Najeriya, ya halarci taron rantsar da shugaban Chadi, Mahamat Déby.
Taron rantsuwar – da aka gudanar a birnin N’Djamena – na zuwa ne bayan hukumar zaɓen Chadi ta ayyana Mahamat Déby Itno a matsayin wanda ya yi nasara a zaɓen.
Shugabvan ya halarci ƙasar tare da wasu manyan muƙarraban gwamnatinsa.
A ranar 18 ga watan Yuni ne kuma, shugaban na Najeriya ya sake halartar wani bikin rantsuwar, amma a Afirka ta Kudu.
A lokacin Tinubu ya tashi ne a filin jirgin saman Legas, tare da gwamnan jihar, Babajide Sanwo-Olu da mataimakin gwamnan jihar, Obafemi Hamzat da sauran jam’ian gwamnati.
Tinubu ya halarci rantsar da shugaban Afrika ta Kudun, Cyril Ramaphosa bayan sake zaɓarsa a wa’adin mulki na biyu.
Taron AU
Haka kuma a ranar 20 ga watan Yuli, Shugaba Tinubu ya je ƙasar Ghana domin taron tsakiyar shekara na ƙungiyar haɗin kan ƙasashen Afirka ta AU, da ka agudanar a birnin Accra.
A lokacin ziyarar shugaban ƙasar na tare da ministan harkokin ƙasashen waje, Amb Yusuf Maitama Tuggar, inda suka samu tarba daga jakadan Najeriya a ƙasar, Amb Dayo Adeoye.
A ranar 13 ga watan Agusta ne kuma, Shugaba Tinubu ya kama hanyar zuwa ƙasar Equatorial Guinea domin wata zirarar aiki ta kwana uku.
A lokacin ziyarar – shugaban na Najeriya ya tattauna batutuwan da suka shafi diplomasiyya da tattalin arziki tsakanin Najeriya da ƙasar Equatorial Guinea, ciki har da cimma yarjejeniyar shimfida bututu.
Tinubu ya kammala ziyarar ne ranar 16 ga watan Agusta, inda firaministan ƙasar ya yi masa rakiya zuwa filin jirgin saman birnin Malabo.
‘Bulaguro a sabon jirgi’
Sannan a ranar 19 ga watan Agustan Shugaba Tinubu ya sake saɓa takalmansa zuwa Faransa.
Cikin sanarwar tafiyar da fadarsa ta fitar a lokacin, ta ce shugaban ya yi bulaguron ne cikin sabon jirgin saman da ya saya.
Fadar shugaban ƙasar ta ce an maye gurbin tsohon jirgin da shugabannin ƙasar ke amfani da shi tun lokacin mulkin Olusegun Obasanjo shekara 19 da suka shuɗe.
A ranar 29 ga watan Agustan shekarar ne kuma, shugaban na Najeriya ya kama hanyar zuwa ƙasar China.
Cikin sanarwa tafiyar da fadarsa ta fitar a lokacin, ta ce shugaban zai ya da zango a ƙasar Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa, kafin isarsa birnin Beijin inda zai halarci taron haɗin gwiwar kasuwanci tsakanin ƙasashen Afirka na China.
A lokacin ziyara Shugaba Tinubu ya gana da shugaban ƙasar China, Xi Jinping da kuma shugabannin wasu kamfanonin ƙasar da nufin inganta harkokin zuba jari da kasuwanci tsakanin Najeriya da China.
Bayan ƙare ziyararsa a China daga can Shugaba Tinubu ya zarce Birtaniya, inda ya shafe wasu kwanaki a can.
A lokacin da yake Birtaniyar, shugaban na Najeriya ya gana da sarkin Charles III na Birtaniya, kafin komawarsa Najeriya cikin watan Satumba.
A lokacin ganawar, shugabannin biyu sun tattauna kan batutuwan da suka shafi matakan magance sauyin yanayi, kamar yadda sanarwar fadarsa ta bayyana a lokacin.
Tafiya hutun mako biyu
A ranar 2 ga watan Oktoba ne kuma, shugaban na Najeriya, ya sake komawa Birtaniya, amma a wannan karon a wani ɓangare na hutunsa na shekara na tsawon mako biyu.
Cikin sanarwar tafiyar da fadarsa ta fitar ta ce shugaban zai yi amfani da hutun domin yin nazari kan tsare-tsare tattalin arzikin arziki da gwamnatinsa ke gudanarwa.
A wannan bulaguro ne ‘yan Najeriya suka yi ta raɗe-raɗin cewa shugaban ba shi da lafiya, har ma ya tafi Faransa domin a duba lafiyarsa.
To sai dai a ranar 11 ga watan na Oktoba, fadarsa ta fitar da wata sanarwa da ta ƙaryata batun rashin lafiyar, sai dai ba ta musanta batun cewa ya tafi Faransa ba.
Ta ma kare matakin da cewa, a matsayinsa na wanda ke hutun aiki, yana da damar gudanar da tafiye-tafiyensa na ƙashin kai, ba sai lallai ya zauna a Birtaniya kaɗai ba.
Shugaban ya koma Najeriya ranar 19 ga watan na Oktoba bayan kamma hutun nasa.
Sai kuma a ranar 10 ga watan Nuwamba, shugaban na Najeriya ya sake karkata akalar jirginsa zuwa ƙasar Saudiyya domin halartar taron haɗin kan ƙasashen Larabawa da Musulmai.
A lokacin taron – wanda ya tattauna batun yaƙin Gaza – shugaban na Najeriya ya gabatar da jawabi.
Inda a ciki ya amince da kafa ƙasashe biyu a matsayin masalahar yaƙin Gaza da ya ƙi ci ya ƙi cinyewa.
Mako guda bayan taron Saudiyya, shugaba Tinubu ya tafi ƙasar Brazil ranar 18 gawatan na Nuwamba, domin halartar taron shugabannin ƙasashen G20, mafiya ƙarfin tattalin arziki.
Shugaban – wanda ya je tare da mai ɗakin Sanata Remi Tinubu – ya samu tarba ta musamman daga shugaban ƙasar Brazil.
A lokacin ziyarar, shugaban na Najeriya ya gana da shugabannin ƙasashen daban-daban da hukumomi ciki har da shugabar Asusun IMF domin tattauna batutuwan da suka shafi zuba jari a Najeriya.
Haka ma a ranar 27 ga watan na Nuwamb, shugaban tare da mai ɗakin tasa suka sake hawa jirgi zuwa birnin Paris na ƙasar Faransa.
Cikin ziyarar aikin ta kwanaki uku, shugaban ya tattauana da takwaransa na Faransa, Emmanuel Macron don ƙulla yarjejeniyoyi tsakanin ƙasashen biyu.
Daga nan kuma shugaban na Najeriya ya zarce ƙasar Afirka ta Kudu, domin halartar taron haɗin gwiwar ƙasashen biyu karo 11, kafin ya koma Najeriya, ranar 5 ga watan Disamba.
Masu suka dai na ganin tafiye-tafiye shugaban na yin yawa, lamarin da ya sa zusuek zargin shugaban ƙasar da kashe kuɗaɗen gwamnatin fiye da kima, a daidai lokacin da ƙasar ke kukan matsin tattalin arziki.
To sai dai fadar shugaban ƙasar a lokuta da dama ta sha kare tafiye-tafiyen shugaban da cewa bulaguro ne da ke ƙoƙarin inganta harkokin zuba jari domin haɓaka tattalin arzikin ƙasar, da kyautata danganta tsakanin NAjeriya da ƙasashen duniya.
BBC Hausa