Duk sati ana hada-hadar Naira biliyan 50 a kasuwar shanu ta Wudil – Shugaban kasuwar

Date:

Daga Abdullahi Shu’aibu Hayewa

 

Shugaban riko na kungiyar Kasuwar Shanu ta Wudil, Alhaji Ahmad Dauda, ​​ya ce ana hada-hadar Naira biliyan 50 duk mako a kasuwar.

Alhaji Dauda ya bayyana hakan ne ga manema labarai a Kano ranar Talata, inda ya ce suna samun kudin ne daga shanun da suke sayarwa kuma sukan sayar da shanun da basu gaza miliyan uku ba a kasuwar da take ci a duk ranar Juma’a da Asabar.

Alhall Dauda ya ce ana kawo shanun ne daga Kano da wasu jihohi da suka hadar da Adamawa, Bauchi, Plateau, Taraba, Sokoto, Borno da Yobe .

Talla

Ya ce mafi yawan dabbobin ana fitar da su ne zuwa Kudu-maso-Kudu, Kudu maso Gabas da Kudu-maso-Yamma na Nigeria.

“Kasuwar Wudil ita ce babbar kasuwar shanu a jihar Kano kuma tana daya daga cikin manyan kasuwanni a arewacin Najeriya inda ake hada-hadar kusan Naira biliyan 50 duk ranar Juma’a.

Dalilin da yasa ba za mu fara sayar da man fetur a sabon farashi ba – IPMAN 

“Shanun su kan fara isowa kasuwar daga ranar Laraba a tireloli, manyan motoci yayin da ake fara siyar da su a ranar Juma’a zuwa ranar Asabar,” inji shi.

Shugaban rikon ya yabawa gwamnatin jihar bisa samar da kayayyakin aiki da kasuwar ke bukata wadanda suka hada da magudanan ruwa da fitila mai amfani da hasken rana da kuma bandakuna.

Sai dai ya ce akwai bukatar kara samar da magungunan ruwa a cikin kasuwar Saboda Wahalar da kwastomominsu suke shiga idan lokacin damina ya yi .

Don haka ya roki gwamnati da ta inganta magudanan ruwa domin a samu saukin fitar ruwa a kasuwar .

Dauda ya kuma roki gwamnati da ta samar da ingantaccen tsaro a kasuwar domin kare ta daga barayin da ya ce sun sace makudan kudade daga hannun ‘yan kasuwar a baya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Za mu karawa Limamai, Ladanai da Na’ibansu alawus na wata-wata – Shugaban Karamar hukumar Dala

Daga Sani Idris maiwaya   Shugaban karamar hukumar Dala Alhaji Suraj...

Zargin kisa a R/Zakara: Gwamnatin Kano za ta kafa kwamiti – Waiya

Gwamnatin jihar Kano, ta ce za ta gudanar da...

Majalisar Dokokin Kano ta yi Doka kan masu tufar da yawu da majina a titi

Majalisar Dokokin jihar Kano ta amince da dokar cin...

Sanata Barau zai baiwa dalibai 1,000 tallafin karatu a Kano ta tsakiya da ta Kudu

Daga Aliyu Danbala Gwarzo   Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau...