Ƙungiyar dillalan man fetur ta Najeriya, IPMAN da kuma kamfanin mai na ƙasa wato NNPCL , sun ce za su ci gaba da sayar da man fetur a tsohon farashi har zuwa lokacin da tsohon kayan da suke da shi zai ƙare.
Kamfanin na NNPCL dai ya ce a sabon farashin zai riƙa bai wa dillalan, man a kan naira 899 inda su kuma za su sayar a kan naira 935.
Ƙungiyar dillalan man ta ce a yanzu haka tana ci gaba da tattaunawa da matatar Dangote domin ganin yadda za su soma ɗaukar man a sabon farashin, kamar Alhaji Salisu Ten-Ten, shugaban dillalan na shiyyar arewa maso yamma ya yi BBC bayani
EFCC ta gurfanar da wanda ake da zargi da almundahanar taki a Kano
Idan za a iya tunawa a karshen makon jiya ne Kamfanin Ɗangote da na NNPCL suka sanara da rage farashin man, domin saukakawa al’ummar Nigeriya