Za mu biya kudaden daliban Kano da Ganduje ya gaza biyawa kudin makaranta a Cyprus – Gwamna Abba

Date:

Daga Rukayya Abdullahi Maida

 

Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya dauki matakin magance matsalolin da daliban Kano wadanda gwamnatin Ganduje ta tura karatu kuma suka kasa karbar shaidar kammala karatunsu.

A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa ya aikowa kadaura24 a ranar Litinin, ta bayyana cewa gwamna Yusuf ya yi wata muhimmiyar ganawa da mahukuntan jami’ar Near East da ke Cyprus domin shawo kan lamarin.

Tattaunawar ta mayar da hankali ne kan batun bayar da satifiket ga daliban Kano da suka kammala karatunsu a shekarar 2015 zuwa 2019.

Talla

Da yawa daga cikin wadannan daliban da aka yaye, musamman wadanda suka yi karatu a fannonin aikin likitanci da aikin jinya, sun kasa samun damar yin aikin da suka koya, sakamakon gaza biyan kudin makaranta da gwamnatin Ganduje ta yi.

Gwamnatin Kano ta yi Martani Kan Hana Sarki Sanusi Kai Hakimin Bichi

Gwamnan ya bayyana lamarin a matsayin babban koma-baya, ba wai ga daliban da abin ya shafa ba, har ma da jihar, wadda take da bukatar kwararru jami’an kula da lafiya.

Gwamnana Abba Kabir Yusuf ya ce gwamnatinsa zata biya duk kudaden da ake bin daliban domin su karɓi Satifiket dinsu don su fara amfani da abun da suka koya domin amfanin al’umma.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Bai dace ɗalibai su rika murnar kammala karatu ta hanyoyin da ba su dace ba – Mal Ibrahim Khalil

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa ‎ ‎ ‎Shugaban majalisar Malamai ta jihar Kano...

Budaddiyar Wasika ga Gwamnan Kano kan wanda zai maye gurbin Muhuyi Magaji R/gado daga Kungiyar Lauyoyi yan Kano

Zuwa ga Mai Girma Alhaji Abba Kabir Yusuf Gwamnan Jihar Kano Gidan...

Dan majalisa Bichi ya sake biyan kuɗin makarantar dalibai 121 masu karatun digiri na biyu da na digirin digirgir

Ɗan Majalisar Wakilai mai wakiltar Mazabar Bichi a Majalisar...