Zaɓen Kano tarihi ne ya maimaita kansa – Kwankwaso

Date:

Jagoran jam’iyar NNPP a Nigeria, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya ce zaɓen ƙananan hukumomin da jam’iyarsa ta gudanar a Kano tarihi ne ya maimaita kansa, “Ba a daki kowa ba, ba a zagi kowa ba, babu wani faɗace-faɗace.”

BBC Hausa ta rawaito Kwankwaso ya ce sun san cewa jam’iyun hammaya na iya daukar matakin shari’a shiyasa suma ba su bari an bar su a baya ba.

“Hukumomin Kano sun san halin wadansu musamman ƴan APC, shiyasa hukumar garzaya kotu saboda ta samu kariya, daman an sanya rai za ayi irin wannan, aka bada hukunci mai ƙwarin gaske wanda ya sanya wa duk wanda zai kawowa dimokradiyya cikasa takunkumi,” Cewar Kwankwaso.

Talla

Sanata Rabi’u Musa ya ce duk wadanda suke ƙoƙarin rikita jam’iyyar hadin baki ne domin a haifar masu da rudani da rikici cikin jam’iyarsu.

A yau Litinin ne ake sa ran shugabannin ƙananan hukumomin jihar Kano 44, za su shiga ofis domin fara aiki gadan-gadan, bayan Gwamna Abba Kabir Yusuf ya rantsar da su a ranar Lahadi.

Hakikanin abin da ya faru dangane da cire Abdullahi T Gwarzo daga Minista – Adamu Abdullahi

An gudanar da bikin rantsarwar a fadar gwamnatin jihar, a gaban manyan ƙusoshin gwamnatin jihar da wakilin sarkin Kano da sarakunan Gaya da Rano da Karaye

Zaɓen jihar Kano na ƙarshen makon jiya, ya zo da matuƙar taƙaddama, inda babbar jam’iyyar adawa a jihar, wato APC ta samo umarnin kotu da ya rusa shugabancin hukumar zaɓen Kano.

Hukumar zaɓen jihar ta bayyana jam’iyyar NNPP mai mulkin jihar da lashe zaɓen duka shugabannin ƙananan hukumomin jihar 44 da kansiloli 484.

Jami’iyyar APC mai hamayya a jihar ba ta shiga zaɓen ba.

A ranar Talatar ne wata babbar Kotun tarayya a kano ƙarƙashin jagorancin mai shari’a Simon Amobeda ta rushe shugabancin hukumar zaɓe ta jahar Kano bisa dogaro da hujjojin da aka gabatar mata na rashin cancantar shugabannin hukumar bisa kasancewarsu ƴan siyasa masu ɗauke da katin Jam’iyyar NNPP.

Wani ɗan jam’iyyar APC Hon Aminu Tiga da Jam iyyarsa ta APC ne dai suka shigar da ƙara inda suka roƙi kotun da ta rushe shugabannin hukumar zaɓen ta Kano bisa kasancewrsu ƴan jam’iyya mai mulki.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Kungiyar cigaban Ilimi da gyaran tarbiya ta unguwar zango ta shirya taron kan tarbiyya da tsaro

Daga Rahama Umar Kwaru   Wani Malami a jami'ar Bayero dake...

Gwamnatin Kano ta sanar da Ranar Fara hutun zangon Karatu na 3 ga ɗaliban jihar

Daga Rukayya Abdullahi Maida   Gwamnatin Jihar Kano ta sanar da...

Gwamnatin Kano za ta fara jiyo ra’ayoyin al’umma kafin gudanar da duk wani aiki a jihar – Bilkisu Indabo

Daga Samira Hassan   Gwamnatin jihar Kano ta sha alwashin nan...

Kwankwaso ya gana da Tinubu a fadar shugaban kasa

Daga Nasiba Rabi'u Yusuf   Tsohon gwamnan jihar Kano, Rabiu Kwankwaso,...