Bayo Onanuga, mai ba da shawara na musamman kan yada labarai ga Shugaba Bola Tinubu, ya ce zarge-zargen da suka danganta Bello Matawalle da hannu a ayyukan ‘yan fashin daji a yankin arewa maso yamma sun bayyana ba gaskiya ba ne.
Matawalle shi ne karamin ministan tsaro. An bar shi a ofis yayin da Tinubu ya yi garambawul ga majalisar ministocinsa a ranar 23 ga Oktoba.

TheCable ta rawaito cewa yayin da ya ke magana a wata hira da Arise TV a ranar Laraba, Onanuga ya ce ba a kori Matawalle, tsohon gwamnan Zamfara, ba saboda ofishin mai ba bawa shugaban kasa shawara kan tsaro ya binciki zarge-zargen da suka shafi alakarsa da ‘yan fashin daji kuma suka gano ba su da tushe.
Onanuga ya ce zarge-zargen da ake yi wa Matawalle “kawai ƙirƙira ne” kuma suna da alaka da siyasa.
Cire T-Gwarzo daga Minista: Bashir Gentile ya aikawa Tinubu Sako
“Gwargwadon abin da na sani, yawancin waɗannan abubuwan zarge-zarge ne kawai,” in ji mai taimaka wa shugaban ƙasar.
“A cikin ɗayansu, na samu wani abu makamancin haka na aika wa Ribadu na tambaye su: ‘Kun ji labarin wannan?’
“Mai bai wa shugaban kasa shawara ya ce: ‘A’a. Mun binciki yawancin waɗannan abubuwan; ba gaskiya bane’. Mutane dai suna fitowa da nau’ikan abubuwan ƙarya da zarge-zarge. Shi ya sa mutumin (Matawalle) har yanzu yana cikin majalisar ministocin.

“Shugaban ƙasa, ina da tabbacin, ya ji labarai da dama game da shi. Domin yana nan a wurin ya nuna cewa… kamar yadda na faɗa, an binciki wasu daga cikin waɗannan abubuwan; an gano ba gaskiya ba ne.
“Ofishin NSA ya riga ya binciki wasu daga cikin waɗannan zarge-zargen. Kawai ƙirƙira ne.”