Dambarwar Hisbah da Murja Kunya: Kotu ta yanke hukunci

Date:

Babbar Kotun jihar Kano mai lamba 11 karkashin mai shari’a Nasir Saminu ta yanke hukunci kan karar da Murja Ibrahim Kunya ta kai Hukumar Hisbah da Kwamishian Yan Sandan Kano da Asibitin Dawanau da kuma alkalin kotun shari’ar Musulunci ta Kwana Hudu.

Majiyar kadaura24 ta Freedom Radio ta rawaito mai shari’a Nasir Saminu ya ce, Hukumar Hisbah ba ta da hurumin kame ko bincike ko gurfanar da wani mutum a Kotu.

Ya ce, aikin Hisbah shi ne wa’azi, amma batun kama mutane da su ke yi cushensa aka yi, amma ba bu shi a doka.

Cire T-Gwarzo daga Minista: Bashir Gentile ya aikawa Tinubu Sako

Kotun ta kuma yi watsi da gurfanar da Murja da aka yi a Kotun Kwana Hudu inda ta ce hakan ya saba wa doka.

Zaɓen Kananan hukumomi: Hukumar zaɓe ta kano ta bayyana matsayarta kan hukuncin Kotu

Mai Shari’a ya kuma umarci a gaggauta bai wa Murja Kunya wayarta da katin cirar kudinta na ATM.

Talla

Kotun ta kuma umarci Murja Kunya ta biya yan sanda da Asibitin Dawanau Naira Dubu Dari Biyu kowannensu sakamakon ta gaza kawo laifin da suka yi mata a gaban Kotun.

Mai shari’a ya kuma umarci Kwamishinan Yansanda ya kama Murja Kunya idan ta aikata wani laifi na yaɗa abin da ya saɓa wa addini da al’ada.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

ALGON ta Kano Sa’adatu Soja ta sami sabon matsayi a kungiyar ALGON ta Ƙasa

Daga: Aliyu Danbala Gwarzo. Shugabar karamar hukumar Tudunwada kuma ALGON...

Da dumi-dumi: Tinubu zai zo Kano

Shugaban Kasa Bola Ahmad Tinubu zai zo Kano ranar...

Tinubu ya sauya sunan jami’ar Maiduguri zuwa Sunan Muhd Buhari

Shugaba Bola Tinubu ya sauya sunan Jami'ar Maiduguri zuwa...

Zargin kwace gona: Majalisar Dokokin Kano zata binciki Shugabar Karamar Hukumar Tudun Wada (ALGON)

    Majalisar dokokin jihar Kano, ta sha alwashin gudanar da...