Yadda Togo da Benin suke samun wutar lantarki sa’a 24 daga Nigeriya

Date:

Manajan darakta kuma babban jami’in gudanarwa na Hukumar Rarraba wutar lantarkin Najeriya TCN, Sule Abdulaziz ya ce ƙasashen Togo da Benin suna samun wutar lantarki ta sa’a 24 daga Najeriya.

“Muna ba Togo da Benin da Nijar lantarki. Suna samun wutar awa 24, kuma suna biya,” in ji Abdulaziz a tattaunawarsa da tashar talabijin ta Channels a ranar Lahadi.

Talla

Da aka tambaye shi dalilin da ya sa ƴan Najeriya da dama ba sa samun wutar kamar haka, sai ya ce, “Yan Najeriya na samun wuta sosai amma ba a ko’ina ba. Waɗanda suke Band A suna samun lantarki na tsakanin awa 20 zuwa 22 a rana,” in ji shi.

Gwamna Abba ya taya Kwankwaso cika shekaru 68 a duniya

Abdulaziz ya ƙara da cewa, “ina tabbatar muku za mu iya fara samun isasshiyar wutar lantarki nan da shekara biyar. Sabon ministan yana ƙoƙari domin tabbatar da hakan.”

Ya ƙara da cewa akwai bambanci tsakanin TCN da Nepa, “lokacin da muke Nepa, mu ne muke samar da wutar, mu rarraba, sannan mu yi kasuwancinta, amma yanzu rarraba wutar kawai muke yi,” in ji shi. Sannan ya ƙara da cewa idan aka samu tangarɗa daga babban layin ƙasar, ana ɗora musu laifi ne saboda ana musu kallon Nepa.

Talla

“Idan an samu tangarɗa ba dole ta zama daga TCN ba, domin za a iya samu a sauran ɓangarorin.”

Shugaban na TCN ya kuma bayyana lalacewar kayan aiki, a matsayin wata matsala da ke addabarsu, inda ya ce, “yawancin kayayyakin aikin da muke amfani da su sun haura shekara 50.”

Talla

A game da tsadar lantarki kuwa, Abdulaziz ya ce, wutar lantarki na da sauƙi a Najeriya, idan aka kwatanta da wasu ƙasashen Afirka irin su Burkina Faso da Senegal da Jamhuriyar Nijar.

BBC Hausa

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Da dumi-dumi: Tinubu ya Iso Kano domin ta’aziyyar Dantata

Shugaban Nigeria Bola Ahmad Tinubu ya iso jihar Kano...

ALGON ta Kano Sa’adatu Soja ta sami sabon matsayi a kungiyar ALGON ta Ƙasa

Daga: Aliyu Danbala Gwarzo. Shugabar karamar hukumar Tudunwada kuma ALGON...

Da dumi-dumi: Tinubu zai zo Kano

Shugaban Kasa Bola Ahmad Tinubu zai zo Kano ranar...

Tinubu ya sauya sunan jami’ar Maiduguri zuwa Sunan Muhd Buhari

Shugaba Bola Tinubu ya sauya sunan Jami'ar Maiduguri zuwa...