Daga Sumayya Kabara
Daruruwan mutane ne a garin Chiromawa da ke Karamar Hukumar Garin Mallam, sun dakile yunkurin sace wani Dattijo mai suna Yusuf Nadabo Mai kimanin shekaru 80 a Duniya.
Alhaji Nadabo, wanda ya mallaki gidan mai na Chiromawa, yana kuma rike da sarautar gargajiya ta Sarkin Noman Kano.
DAILY NIGERIAN ta rawaito cewa masu garkuwa da mutanen Waɗanda Suke dauke da makamai sun kai farmaki ofishin Alhaji Nadabo ne da ke gidan man sa wanda ke Bakin Tasha a ranar Juma’a da karfe 7:35 na yamma, inda suka rika harbin iska don tsorata mutanen dake Wajen.
A cewar majiyoyinmu, daya daga cikin mutanen yankin ya samu raunika a dalilin harbin a kokarin sa na tunkarar maharan.
Masu garkuwa da mutanen ba su yi sa’a ba, Saboda sun zo ranar kasuwa, kuma akwai jama’a da dama da suke harkokinsu a yankin,” kamar yadda wani ganau ya shaida wa DAILY NIGERIAN.
“Lokacin da suka yi garkuwa da shi da dansa Isyaku, sai suka fara tafiya da su zuwa Bakin wata makabarta. inda scan ne suka boye baburan da Suka zo da su. Amma mutanen wajen suka bijirewa karar harbe-harben Suka tunkaresu Suna fadin ‘Allahu Akbar’.
“Yayin da harsashin bindigarsu suka kare, kuma Alhaji Nadabo ya kasa tafiya da sauri saboda tsufa, sai suka karbi Naira 80,000 da suka samu a aljihunsa suka gudu.”a cewar Wani Wanda abun ya faru a Kan idonsa
Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Kano, Abdullahi Kiyawa, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce ‘yan sanda tare da hadin gwiwar al’umma da ’yan Vigilantee ne suka dakile garkuwa da Dattijo n.”
An kai rahoton lamarin ga ‘yan sanda da misalin karfe 7:57 na yammacin ranar Juma’a, kuma mun yi gaggawar tura ‘yan sanda zuwa yankin, Tare da hadin guiwar ‘yan Vigilantee na yankin, da kuma al’ummar yankin, muka Sami nasarar dakile Sarkin noman,” in ji Kiyawa.