Likitocin Kano sun bayyana dalilinsu da ranar tafiya Yajin aiki

Date:

 

 

Likitoci a Jihar Kano, sun bayyana damuwarsu kan rashin isassun likitocin da za su ke duba marasa lafiya, wanda hakan ya sa suke shirin tafiya yajin aiki daga ranar 1 ga watan Oktoba.

Ƙungiyar Likitocin Asibitocin Gwamnati da Likitocin Haƙora ta Ƙasa ce, ta bayyana hakan, yayin wani taron manema labarai da sakataren ƙungiyar, Dokta Anas Idris Hassan, ya jagoranta.

Talla

Ya ce gwamnatin jihar ta amince a watan Yuni za ta biya musu buƙatunsu, amma har yanzu ba ta ɗauki wani mataki ba.

Ɗaya daga cikin muhimman batutuwan da suke korafi a kai shi ne rashin biyansu alawus bayan wucewar annobar COVID-19, wanda Gwamnatin Tarayya ta biya tun a 2021, amma Gwamnatin Jihar Kano har yanzu ba ta biya ba.

Talla

Dokta Anas ya kuma bayyana cewa likitocin da aka ɗauka aiki a watan Satumban 2023 ba su samu albashinsu ba.

Likitocin sun kuma koka kan yanayin asibitocin Kano da rashin manyan kayan aiki.

An kori wani ɗan siyasa daga gidansa bayan da matarsa ta jinginar da shi ta ciyo bashi

Babbar matsalar ita ce ƙarancin likitocin da za su ke duba marasa lafiya.

A Kano, akwai kimanin mutum miliyan 20, amma likitoci 600 ne kawai suke duba su, wanda hakan ke nufin likita ɗaya na kula da marasa lafiya 33,000.

Talla

Wannan adadi ya saɓa da ƙa’idar da Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta tsara.

Saboda waɗannan matsaloli, likitocin suka yanke shawarar tafiya yajin aiki daga ranar 1 ga watan Oktoba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Iftila’i: Almajirai 17 sun kone kurmus 15, sun jikkata sanadiyya wata gobara

Daga Maryam Muhammad Ibrahim   Wata gobara da ta tashi ta...

Mun gano yadda yan Bauchi ke mamaye dazukan Kano – Gwamnatin Kano

Daga Nazifi Dukawa     Gwamnatin jihar Kano ta ce ta gano...

Gwamnatin Kano Ta Kammala Aikin Gina Mayanka ta Naira Biliyan 1.5

Daga Zakaria Adam Jigirya     Gwamnatin jihar Kano ta karkashin Shirin...

An dakatar da Shugaba da Sakataren kungiyar APC X Eagle forum

Kwamitin zartarwa na kungiyar APC X Eagle forum ya...