Daga Habiba Bukar Hotoro
Kamfanin shirya fina-finai na Uk entertainment ya maka fitacciyar jarumar Kannywood, Hafsat Idris wadda akewa lakabi da Barauniya a gaban kotu bisa zargin Saba alkawarin da Suka kulla fa Kamfanin.
A karar da Kamfanin ya shigar gaban babbar kotun Kano Mai lamba 14 da ke zamanta a karamar hukumar Ungogo, an zarge jarumar da karbar Naira miliyan 1.3 domin ta fito a cikin wani Shiri Mai Dogon zango amma ta gagara cika alkawarin yin aikin Kamar yadda aka kulla yarjejeniyar da ita kamar yadda jaridar Daily Trust ta rawaito.
Mai shigar da karar ya ce kamfanin yayi asara Mai yawa saboda karya alkawarin da Hafsat Idris ta yi.
Kamfanin shirya fina-finan ya bukaci kotu ta Umarci Hafsat Idris ta bayar da Naira miliyan 10 a matsayin diyyar asarar data jawowo musu.
Wadda ake tuhuma, ta hannun lauyanta, ta gabatar da martani na musamman kan da’awar.
Kotun ta dage sauraren karar.
Wacece Hafsat Idris?
Hafsat Ahmad Idris (an haife ta 14 Yuli 1987) yar wasan fina-finan Kannywood ce a Najeria.
Ta fito a fim dinta na farko mai suna Barauniya a Shekarar (2016).
Ta Jarumar Shekara 2019 a Cikin takwarorinta Mata dake a masana’antar Kanywood.