Daga Mardiyya Ahmad Daneji
Shugaban masu rinjaye na majalisar wakilai ta kasar nan kuma dan majalisa mai wakiltar kananan hukumomin Tudun wada da Doguwa Hon. Alhassan Ado Doguwa ya bayyana cewa babban taron yan majalisun kasashen Africa zai haifar da kyakykyawan sakamako ga al’ummar Africa baki daya.
Shugaban masu rinjayen ya bayyana hakan ne yayin babban taron yan majalisun kasashen Africa wadanda suke rainon ingila, wanda Nigeria take daukar nauyinsa yanzu haka a babban birnin tarayya Abuja.
Alhassan ado wanda shi ne Sardaunan Rano yace dama akan shirya taron a lokuta daban-daban ,inda ake tatattaunawa kan muhimman batutun da zasu tallafawa rayuwar al’ummar Africa baki daya.
Yace taron wanda shi ne karo na 51 zai mai da hankali ne wajen inganta wakilcin da yan majalisu suke yiwa al’ummar da kuma samar da hadin kan yan majalisun kasashen Africa da kuma tabbatar da yin dokoki wadanda zasu inganta rayuwar al’ummar da suke yiwa wakilci.
” Majalisar kasar nan ce ta dauki nauyin taron kuma dama haka ake, kamar yadda akai a kasashen Ghana Camaroon da dai sauran Manyan kasashen Africa, an tattauna matsalolin da suke addabar kasashen Africa musamman ta’addaci, shaye-shayen miyagun kwayoyi, da matsalolin da Demokaradiyya take fuskanta musamman batun juyin mulki da ake samu a wasu kasashen Africa a baya-bayan nan” . inji Doguwa
Alhassan Doguwa ya yi fatan a karshen taron dukkanin yan majalisun da suka halacci taro zasu kara samun gogewa ta yadda zasu ingata aikinsu don amfanin al’ummarsu.