Ɗangote ya ce ya yi da-na-sanin kin siyan Arsenal

Date:

 

 

Shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Alhaji Aliko Dangote ya ce yanzu lokaci ya wuce da zai saya ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Arsenal da ke Ingila, inda ya ce zai cigaba da zama mai goyon bayan ƙungiyar a duk lokacin da take wasa.

Dangote ya bayyana hakan ne a tattaunawarsa da Bloomberg, inda ya ce yana kallon wasannin ƙungiyar sosai.

“A zantawarmu ta baya na ce da zarar na kammala aikin gina matatar man fetur ɗina zan koma batun sayan Arsenal. Amma yanzu lokacin wannan maganar ya wuce domin komai yanzu ya yi tsada, sannan yanzu ƙungiyar tana ƙoƙari sosai, amma a wancan lokacin da na yi maganar ƙungiyar ba ta kan ganiya.”

Talla

Da aka tambaye shi ko ya yi da-na-sanin rashin sayan ƙungiyar a wancan lokacin, sai ya ce, “gaskiya na yi da-na-sani, amma kuma a lokacin na fi buƙatar kuɗin wajen kammala aikin da na ɗauko na gina matatar man fatur ɗin nan sama da sayan Arsenal ɗin. Da na saya ƙungiyar a lokacin a kan kuɗi $2, amma kuma wataƙila da ban kammala aikin matatar ba. A lokacin zaɓin ko dai in kammala aikin gina matatar ne, ko kuma in saya Arsenal.”

Hukumar lafiya ta bayyana adadin yara da matan da suke mutuwa kullum a Nigeria

A shekarar 2020 ce Dangote ya bayyana ƙudurinsa na sayan ƙungiyar ta Arsenal da zarar ya kammala aikinsa na gina matatar men fetur.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gyaran tarbiya: Makarantun Islamiyya na taka muhimmiyar rawar gani

Daga Zakariyya Adam Jugirya   Wani Malamin addinin musulunci a Kano...

Fadar shugaban ƙasa ta mayar da martani ga Kalaman Kwankwaso

Fadar Shugaban Ƙasa ta musanta zargin Sanata Rabiu Musa...

Yadda Kwamishina a gwamnatin Kano ya tsayawa wani dilan ƙwaya aka bada belin sa a kotu

  Kwamishinan Sufuri na Jihar Kano, Ibrahim Namadi, ya tsaya...

Kwankwaso ya caccaki gwamnatin Tinubu

  Tsohon gwamnan jihar Kano, Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso ya...