Daga Maryam Muhammad Ibrahim
Gwamnatin tarayya ta bayyana wadanda ya kamata su amfana da shinkafar da zata sayar da kuma hanyoyin da za a abi domin mallakar Shinkafar akan farashin Naira dubu 40 kowanne buhu.
Kadaura24 ta rawaito Dr. Haruna Sule shi ne daraktan tsare-tsare na ma’aikatar aikin gona ta kasa , ya yi bayani dalla-dalla kan yadda al’umma za su amfani shirin.
YANZU-YANZU: Tinubu ya magantu kan karin farashin man fetur Nigeria
Idan za’a iya tunawa kadaura24 ta rawaito cewa gwamnatin tarayya ta fara sayar da Shinkafar akan farashin naira dubu 40 kowanne babban buhu domin saukakawa al’umma.
Dr. Haruna Sule ya ce masu karamin karfi da ma’aikatan gwamnatin ne zasu amfana da tsarin sayar da Shinkafar na gwamnatin tarayya.
Ya ce dole ne duk wanda ya ke so ya sayi Shinkafar ta gwamnatin tarayya ya zamana yana da lambar katin shaidar dan kasa wato NIN.
Ya ce su kuma ma’aikatan gwamnati za iya siyan Shinkafar ne da lambarsu ta tsarin biyan albashi wato IPPIS.
” Za a biya kuɗin Shinkafar ne ta na’urar ATM Ko Turawa ta banki, sannan duk wanda ya biya za a bashi wata lamba wadda shi kadai yake da ita, ita ce a matsayin shaidar ya biya kuma ita zai nuna ya karɓi Shinkafar da ya siya”.
Man Fetur shi zai rika yiwa kansa farashi yanzu a Nigeriya – NNPC
Dr. Haruna Sule ya kuma ce za a samar da Wuraren sayar da Shinkafar a duk fadin jihohin Nigeria har da Babban birnin tarayya Abuja.