Daga Maryam Muhammad Ibrahim
Wata kungiya mai zaman kanta mai zaman kanta, mai suna One Voice Initiative, ta sanar da sunayen shugabannin kungiyar na Nigeria.
Kungiyar One Voice Initiative kungiya ce mai fafutukar inganta shugabanci nagari, da rikon amana, da ci gaban harkokin siyasa, a Nigeriya.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun Daraktan hulda da jama’a na kungiyar Abubakar Abdulkadir Dangambo.
Yanzu-yanzu:Kotu ta baiwa hukumar zaben Kano umarni Kan zaben kananan hukumomi
Ga jerin sunayen Shugabannin kungiyar na kasa:
1. Abbas Abdullahi, cissp,ipma: Shugaban kungiyar na ƙasa
2. Comr. Sani Garba: Daraktan harkokin sadarwa
3. Khadija Muhd: Darakta Kan al’amuran da suka shafi samar da daidaito (Jinsi)
4.Ali Maiwada: Daraktan Tsare-Tsare:
5. Nura Saghir Muhd: Daraktan kula da harkokin Siyasa da Jam’iyyu
6. Malam Abubakar Abdulkadir Dangambo: Daraktan hulda da manema labarai
Kotu ta tusa keyar alƙalin bogi zuwa gidan yari a Kano
7. Hajiya Hindatu Bashir: Daraktar Tuntuba
8. Hajiya Hauwa Muhd: Daraktar harkokin kudi da walwala
9.Comr. Auwal Ali : Darakta kan harkokin Ƙungiyoyi
10. Alhaji Lawan Muhammad Riba: Kuma shugaban kwamitin amintattu
Dukkanin waɗannan mukamai kowa an bashi ne bisa kwarewarsa a fannin da aka bashi mukamin akai.