Shugaban majalisar gudanarwar Kungiyar tuntuba ta arewacin Najeriya wato ACF, Alhaji Bashir Dalhatu ya nemi gafarar ‘yan arewacin kasar saboda abinda ya kira gazawar su wajen kare yankin daga fadawa rikici mafi muni a tarihinsa.
Dalhatu ya ce suna ci gaba da lalubo hanyar shawo kan Waɗannan matsaloli da suka yiwa yankin kamun kazar kuku.
Karin Farashin Mai: Ya kamata yan majalisu su takawa NNPC burki – Gidauniyar GCAF
Shugaban ya ce yankin arewacin kasar zai rungumi shirin sake fasalin kundin tsarin mulki da jagorancin Najeriya domin ci gaba da kare darajar da martabar yankin.
A jiya laraba ne dai wasu daga cikin shugabannin yankin suka gudanar da mahawara a kan matsalolin da suka addabi yankin.
Kungiyar Samarin Tijjaniyya sun Allah wadai da kara kudin man fetur a Nigeria
Cikin masu halartar taron harda tsohon Sakataren gwamnati Yayale Ahmed da Janar Halilu Akilu da Janar Muhammad Magoro da Tsohon Sufeto Janar MD Abubakar da tsoffin sakatarorin gwamnati Babacir Lawal da Boss Mustapha da kuma tsofin gwamnoni irin su Sule lamido da Adamu Muazu da Ibrahim Shekarau da Ali Sa’ad Birnin Kudu dai sauransu.
Daily trust