Rukayya Abdullahi Maida
Gwamnan jihar kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya tabbatar wa da Abubakar Adamu Rano kujerar shugaban gidan Radio Jihar Kano.
Idan za’a iya tunawa kadaura24 ta rawaito cewa a ranar 22 ga watan Disamba, 2024, gwamnan jihar kano ya baiwa Abubakar Rano umarni kula da gidam Radiyon, sakamakon dakatar da tsohon shugaban gidan Radio.
Zanga-zanga: Gaskiyar magana kan sakin Turawan da ake zargi da hannu a ɗaga tutar Rasha a Najeriya
Kafin bashi rikon kwaryar kula da gidan Radio Jihar Kano, Abubakar Adamu Rano ne mataimakin shugaban gidan Radio.
Rahotanni dai na nuni da cewa gwamnan jihar kano ya amince da irin rawar da Abubakar Adamu Rano ya taka a matsayinsa na mai rikon mukamin shugaban gidan Radio Jihar Kano.
Abubakar Adamu Rano ya samar kayan aiki tare da inganta jin dadi da walwalar ma’aikatan gidan Radio Jihar Kano.