Magance talauci: Shugaban Kano Poly yana ba da tallafin Naira dubu 100 ga al’ummar D/Tofa kowanne wata

Date:

Daga Musa Mudi Dawakin Tofa
Mazabar Kwa dake yankin Karamar hukumar Dawakin Tofa ita ce mazaba ta hudu cikin mazabu goma sha daya da al’ummarta suka amfana da tallafin Shugaban Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta jihar Kano Dokta Kabir Bello Dungurawa a ranar Lahada 7/11/2021.
A yayin taron bada tallafin Dr Kabiru Dungurawa ya ce suna zabo mutane ashirin marayu da marasa karfi maza da mata ne don basu tallafin, kuma mazabar Kwa ita ce mazaba ta huda ta amafana a wannan rana cikin mazabun dake karamar hukumar Dawakin tofa.
Dr Kabir Bello Dungurawa ya kara da cewa la’akari da halin matsin rayuwa da al’ummar karkara ke ciki yasa Gwamna Kano ya basu dama ta shugabanci, saboda haka a duk karshen wata “nake cire naira dubu dari daga albashinna don tallafawa mabukata ashirin a kowacce mazaba dake karamar hukumarta”.
“Ina fatan wannan ɗan tallafi zai taimakawa wadanda suke amfana da tallafin wajen inganta rayuwar da ta makusantansu”. inji Dr Dungurawa
Kungiya Malamai makarantun gaba da sakandire ‘Yan asalin karamar hukumar Dawakin Tofa su aka dorawa alhakin zakulowa tare da tantance duk waɗanda za su amfana da tallafin.
 Wakilin Shugaban Kungiyar malaman wanda kuma shi ne Ma’ajin Kungiyar Malam mai suna malam Junaidu Dalladi ya ce sun zabo marayu, nakassu da masu karamin karfi don basu tallafin, ya kuma yi kira ga duk wadanda suka amfana da tallafin kudin  da su yi amfani dasu ta hanyar da ta dace.
Malam Junaidu Dalladi ya kuma yi kira ga duk masu hali da suya koyi da tallafin dan Kungiyarsu wato Dokta Kabir Bello Dungurawa don ragewa al’umma raɗaɗin halin matsi da ake ciki.
Taron bada tallafin ya gudana a makarantar Firamare dake garin Kwa yankin karamar hukumar Dawakin Tofa a masarautar Bichi.
Al’ummar garin kwa musamman waɗanda suka ci gajiyar tallafin sun godewa Dr Kabiru Dungurawa bisa wannan tallafi ,tare da bada tabbacin zasu yi amfani da tallafin ta hanyar da ta dace.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Yanzu-yanzu: An zabi sabon shugaban jami’ar Bayero BUK

Daga Rahama Umar kwaru   Farfesa Haruna Musa ya zama sabon...

An sake sauya lokacin jana’izzar Aminu Ɗantata – Gwamnatin Nigeria

Gwamnatin tarayyar Nigeria ta ce Hukumomi a Kasar Saudiyyar...

Fadan daba: ku fito ku Kare Kan ku da iyayenku – Gwamnatin Kano ga matasa

Ku tashi ku Kare kanku da iyayen Gwamnatin jihar kano...