Tinubu ya amince da korar duk wanda aka ɗauka aiki da Digiri dan Kwatano

Date:

 

Gwamnatin tarayya ta amince da korar ma’aikatan gwamnati da masu zaman kansu da aka ɗauka aiki da takardar shaidar kammala digiri na bogi da aka samo daga jamhuriyar Benin da Togo, wanda aka fi sani da Digiri dan Kwatano.

Ministan Ilimi, Tahir Mamman, wanda ya bayyana hakan a yayin wani taron manema labarai na murnar cika shekara guda a kan muƙamin a Abuja a jiya Juma’a, ya ce an amince da matakin ne a wani taron majalisar zartarwa ta tarayya da aka yi kwanan nan, wanda shugaba Bola Tinubu ya jagoran ta.

Ya ce matakin na daga cikin shawarwarin kwamitin da gwamnatin tarayya ta kafa domin binciken wani rahoto na sirri da DAILY NIGERIAN ta wallafa a watan Disamba.

Talla
Talla

Rahoton ya fallasa yadda wani wakilin jaridar DAILY NIGERIAN mai suna Umar Audu ya samu takardar shaidar digiri daga jami’ar Ecole Superieure de Gestion et de Technologies, ESGT, Cotonou, Jamhuriyar Benin cikin kasa da watanni biyu.

Sarki Aminu ya bar Kano a karon farko bayan fara dambarwar masarautar

Ya kuma yi amfani da takardar shedar digirin shiga shirin yi wa kasa hidima na NYSC, duk da cewa ya taba yin shirin bayan kammala digirin sa na ainihi kusan shekaru biyar da suka gabata.

Sai dai kuma Mamman, ya ce galibin makarantun da daliban Najeriya daga kasashen biyu ke halarta ba su da lasisi.

Sabuwar Badakala a Kano: An kama Kantomomi 3 da wasu 19, An kuma Saki Dan Kwankwaso

“Don haka a karshe, abin da gwamnatin tarayya ta amince da shi shi ne, sakataren gwamnatin tarayya, SGF, zai fitar da wata sanarwa ga dukkan ma’aikatu, na gwamnati ko na masu zaman kansu, don fitar da duk wani da ke da takardar shedar digiri daga wadannan jami’o’i na bogi.

“Shugaban ma’aikata kuma, an umurce shi da ya zakulo duk wanda ke da wannan takardar shaidar digiri daga wadannan jami’o’i a cikin ma’aikatan gwamnati.

“Don haka wannan shine matakin gwamnatin tarayya akan wannan batu,” in ji ministan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Yanzu-yanzu: Naja’atu Muhd ta mayarwa da Nuhu Ribado Martani Kan barazanar da ya yi mata

Daga Isa Ahmad Getso   Yar gwagwarmayar nan Hajiya Naja'atu Muhammad...

Zargin Sharrin: Ribado ya yi barazanar maka Naja Muhammad a Kotu

Daga Maryam Muhammad Ibrahim   Mai baiwa shugaban kasa shawara kan...

Rusau: Kwankwaso ya bukaci gwamnan Kano ya biya diyyar mutanen da aka kashe a Rimin Zakara

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa   Jigon jam’iyyar APC a jihar Kano,...

Za mu karawa Limamai, Ladanai da Na’ibansu alawus na wata-wata – Shugaban Karamar hukumar Dala

Daga Sani Idris maiwaya   Shugaban karamar hukumar Dala Alhaji Suraj...